MATSALAR TSARO: Kiran APC Na A Sanya Dokar Ta-baci A Zamfara Shirme Ne, Da Raina Al’ummar Jihar Zamfara – PDP A Zamfara

Jami’iyyar PDP a Jihar Zamfara, ta bayyana kiran da jam’iyyar APC ƙarƙashin jagorancin tsohon Gwamnan jihar Bello Matawalle da Sanata Abdulaziz Yari suka yi na kafa dokar ta-baci a Zamfara a matsayin “hassada” da ci gaban da aka samu a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal.

A wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran Jami’iyyar PDP na Zamfara, Halliru Andi ya fitar a ranar, 22 ga Satumba, 2024, ta ce, “Gwamnatin PDP ta mayar da hankali ne wajen gyara kura-kuran da aka tafka a mulkin APC na tsawon shekaru 25, kuma a bayyane yake cewa jam’iyyar APC na shakkar Gwamna Lawal. Yunƙurin da suka yi na zagon ƙasa ga ƙoƙarinsa na nuna matuƙar buƙatar ceto harkokin siyasarsu yayin da zaben 2027 ke gabatowa.”

Ta ce, “Kiran a kafa dokar ta-baci ba shi da tushe balle makama kuma rashin mutunta al’ummar jihar Zamfara ne. Jam’iyyar APC ta yi biris da abubuwan da suka shafi tsohon Gwamna Bello Matawalle, wanda rashin sanin makamar aikin sa ya ƙara dagula harkar tsaro a jihar.”

“Rashin tabbatar da tsaro da gwamnatinsa ta yi ya samo asali yayin da ta rinƙa ƙirƙirar samar wa ’yan ta’adda da wurin zama da sunan “sulhu”, ciki har da bayar da motocin Hilux da kuma tukuicin kuɗi ga ’yan bindigar, tare da ba su damar shiga gidan gwamnati kai tsaye. Wannan ya sa al’ummar Zamfara suka gamu da mugun nufi na wannan sakaci, inda ’yan bindiga ke afka wa al’umma su koma su noƙe a bayan masu masu mulki.

“Ikirarin rashin gaskiya na cewa Gwamna Dauda Lawal na yin zagon ƙasa a yaƙin da ake yi da ’yan bindiga a Jihar Zamfara, wani yunƙuri ne na siyasa domin kawo cikas ga ƙoƙarin da muke yi na magance matsalar rashin tsaro a jihar,” in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa, “Gwamna Lawal shi ne na farko a tarihin jiharmu da ya ba da fifiko kan harkokin tsaro tare da jajircewa na gaskiya, sabanin yadda gwamnatocin APC da suka shuɗe suka yi.”

“Ba kamar jam’iyyar APC da ta siyasantar da matsalar rashin tsaro ba, gwamnatin PDP ta himmatu wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Zamfara. Nasarorin da muka samu a kan ‘yan bindiga sun samo asali ne daga jajircewar Gwamna Lawal, na ƙin yin sulhu da masu laifi. Wannan matsaya mai ƙarfi ta kafa tabbataccen alƙibla a yaƙinmu da ‘yan ta’addan.

“Gwamnatin PDP ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta ɗauki muhimman matakai da suka haɗa da kafa Rundunar Tsaron Kare Al’umma ‘Askarawan Zamfara’ (CPG) da kuma samar da asusun kula da tsaro domin tallafawa jami’an tsaro. Makonni kaɗan da suka gabata Gwamna Lawal ya raba motoci domin inganta ayyukan hukumomin tsaro, inda ya nuna jajircewarsa kan wannan lamari mai matuƙar muhimmanci,” in ji sanarwa.

Sanarwar ta ce, “Zargin da APC ke yi farfaganda ce kawai. Ko kaɗan tsohon Gwamna Matawalle bai bayyana aniyar haɗa kai da Gwamna Lawal wajen magance matsalar rashin tsaro ba. Bugu da ƙari, Matawalle, wanda yanzu shi ne ƙaramin ministan tsaro, ya nuna rashin ƙwarewa da kuma tashin tausayawa ga al’ummar Zamfara. Tattaunawar da ya yi a asirce da ’yan bindiga, ba tare da sanin Gwamna Lawal ba, kai tsaye ya ruguza tsayuwar gwamnatin da ta yi hannun riga da batun yin sulhu da ‘yan bindiga. Bayan rashin nasarar wannan tattaunawar, ya yi ikirarin ƙarya cewa Gwamna Lawal ya amince da Naira biliyan 1.3 a cikin wata takarda da aka ƙirƙira domin sulhuntawa da ’yan ta’adda, magana mara tushe.”

Ta ce, “Muna kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya kori Bello Matawalle daga muƙaminsa na ƙaramin ministan tsaro. Rashin amincinsa da rashin cancantar wannan matsayi ya bayyana ƙarara a cikin ayyukan da ya yi a baya, wanda ba kawai ya lalata yaƙin da ake yi da ‘yan binidiga a halin yanzu ba ne, har ma kawo haɗari ga lafiyar ‘yan ƙasarmu. Ya zama wajibi gwamnatin tarayya ta binciki matakan da Matawalle ya ɗauka, musamman alaƙar sa da shugabannin ’yan bindiga, waɗanda ke zama cikas ga shugabanci nagari.”

“A ƙarshe muna kira ga jam’iyyar APC da ta mayar da hankali kan al’amuran da suka shafi jihar Zamfara, maimakon yin tuhume-tuhume da karkatar da hankalin al’umma. Gwamna Dauda Lawal dai ya tsaya tsayin daka kan ƙudirinsa na kawo sauyi a jihar, kuma ba zai sa ya yi ƙasa a gwiwa ba da ikirarin da ‘yan adawa ke yi. Al’ummar Zamfara na buƙatar zaman lafiya, kuma wannan gwamnati ta himmatu wajen ganin ta cika wannan alƙawarin da ta ɗauka,” in ji sanarwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *