Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga membobin ƙungiyar masu saka tallace-tallace a kafafen yaɗa labarai da su mayar da hankali wajen faɗakar da ‘yan Nijeriya kan sababbin tsare-tsaren tattalin arziki waɗanda gwamnatin Tinubu ta zo da su, waɗanda burin su shi ne haifar da cigaban ƙasa ta fuskar tattalin arziki.
Idris ya yi kiran ne ranar Alhamis a Abuja a lokacin buɗe babban Taron Masu Tallace-tallace na Ƙasa mai taken “Sadarwar Talla a Matsayin Mai Kawo Nagartaccen Sauyi Ga Ƙasa”.
A cewar hadimin musamman na ministan kan yaɗa labarai, Malam Rabi’u Ibrahim, ministan ya samu wakilcin Darakta-Janar na Hukumar Wayar Da Kai ta Ƙasa (NOA), Mista Lanre Issa-Onilu, a taron, kuma ya yi la’akari da muhimmiyar rawar da ƙwararrun masu sana’ar tallace-tallace a kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen yaɗa labaran da za su yi tasiri a wajen jama’a.
Ya ce su na kan cikakken matsayin da za su iya jan akalar samun sauyi a tsarin tattalin arziki da zamantakewar Nijeriya ta hanyar yi wa jama’a yekuwar yadda za su ci moriyar sababbin tsare-tsaren da gwamnatin ke aiwatarwa.
Idris ya ce: “Tun daga ranar farko, Shugaban Ƙasa ya maida hankali – kuma mun ga hakan daga tsauraran matakai wajabtattu da ya ɗauka su kan batutuwan tallafin man fetur, tsarin musanyar kuɗin ƙasashen waje, da sauye-sauyen tsarin tattalin arziki, da ma wasu muhimman abubuwan.
“Mu na sauya tsarin biyan haraji, tare da faɗaɗa Rajistar Zamantakewa ta Ƙasa wadda ta hanyar ta ne ake bayar da tallafi ga ‘yan Nijeriya mafi talauci kuma mabuƙata. Kwanan nan Shugaban Ƙasa ya gabatar da Kasafin Kuɗin sa na shekara na farko ga Majalisar Tarayya, wato Kasafin Sabuwar Fata, wanda ya ɗora fifiko kan samar da ayyukan yi, da farfaɗo da tattalin arziki, daidaita manyan ginshiƙan hanyoyin tattalin arziki, samar da yanayin yin kasuwanci cikin sauƙi, rage fatara, tallafa wa jama’a, da inganta rayuwar al’ummar ƙasa.”
Ministan ya ce Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin tallafa wa ƙananan sana’o’i, da Shirin Shugaban Ƙasa na Bada Rance Bisa Ƙa’idoji da shirye-shiryen rage raɗaɗin rayuwa, waɗanda aka yi domin ‘yan kasuwa, masu aikatau, masu sufuri, ‘yan talla, da masu ayyukan fasaha da bada ƙananan rance.
“Sana’o’i mafi ƙanƙanta a ƙasar nan su miliyan 1 za su ci moriyar rancen kuɗi N50,000 kowannen su, yayin da manyan sana’o’i za su ci moriyar rance daga Asusun Naira Biliyan 75 da aka tanadar.”
Ministan ya ƙara da cewa waɗannan shirye-shiryen ɗori ne a kan waɗanda da ma can an bayyana su kuma ana aiwatar da su, misali samar da motocin safa-safa masu aiki da hasken rana da gwamnatocin jihohi za su ƙaddamar, domin rage wahalar da cire tallafin man fetur ya janyo.
Ya ce duk waɗannan tsare-tsaren ba wai an yi su da ka ba ne, a’a, sai da aka tsara su a tsanake cikin Ajandar Sabuwar Fata ta Shugaban Ƙasa, wadda ta haɗa da sauya fasalin tattalin arziki don a samar da cigaba mai ɗorewa; ƙarfafa tsarin tsaro don samar da kwanciyar hankali da arziki; haɓaka aikin gona don wadata ƙasa da abinci; buɗe hanyoyin makamashi da ma’adinai don samun cigaba mai ɗorewa da kuma bunƙasa hanyoyi da gine-gine a matsayin su na turakun kawo cigaba.
Sauran su ne: bada muhimmanci ga harkokin ilimi, kiwon lafiya, da taimakon jama’a a matsayin muhimman ginshiƙan cigaban ƙasa da gaggauta faɗaɗar hanyoyin tattalin arziki ta hanyar masana’antu, aiki da komfuta, fasahohin zamani, ƙere-ƙere, da ƙirƙire-ƙirƙire.
Ya ce: “Mu na buƙatar samun hanyoyi da salon magance matsaloli na basira daga gare ku, mu na buƙatar yin aiki da hanyoyin da ku ka tsara waɗanda babu kamar su, mu na so mu yi aiki da abubuwan da ku ka tsara. Wannan ba maganar farfaganda ba ce ko surutu, ko kaɗan! Maimakon haka, magana ce ta wayar da kan jama’a, faɗakarwa, da buɗe idanun ‘yan Nijeriya don su ga damarmaki daban-daban da ke ɓullowa a zagaye da su.”
Ministan ya ce wannan gwamnatin ta sadaukar da kan ta ne ga samar da bayanai a kan lokaci kuma ta nagartacciyar hanya, kuma ya bada tabbacin cewa zai gudanar da aikin da aka ɗora masa a buɗe kuma a mutunce.
Ya ce: “A yayin da mu ke bada bayani ba tare da ɓoye komai ba kuma a cikin nagarta, ina kira a gare ku a matsayin ku na ƙwararru da ku tattaro ƙwan ku da kwarkwatar ku ku taimaka mana domin mu isar da bayani dalla-dalla ga jama’a ba tare da wata hargowa ko sauya shi ba.”