Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai ya yi kira ga Hukumar Masu Zanen Gine-gine

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga Hukumar Masu Zanen Gine-gine ta Ƙasa (National Institute of Architects) da su shiga sahun gaba wajen yin azamar farfaɗo da kyawawan fasalin gine-ginen da ke ƙara haskaka tarihin Nijeriya.

Idris ya ce irin waɗannan gine-gine masu fasalin daɗaɗɗen tarihi su ne ke nuna irin ƙasaitar kowace ƙasa.

Mataimakin Daraktan Yaɗa Labarai na Ma’aikatar Yaɗa Labarai, Suleiman Haruna, ya faɗa a cikin wata sanarwa da sa wa hannu, cewa ministan ya bayyana hakan ne a yayin da tawaga daga hukumar ta kai masa ziyara, a ranar Alhamis.

Ya ƙara da cewa akwai buƙatar cibiyar ta himmatu wajen taskace kayayyakin tarihi musamman masu nuna ƙasaitattun gine-gine masu tarihi domin yawancin ‘yan Nijeriya ba su ma san tarihin ƙasaitattun gine-ginen da ke yankunan su ba.

Idris ya ce: “Shin ko kun san cewa ofishin Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA) a yanzu haka a Abuja, ya taɓa zama ofishin  tsohon Shugaban Ƙasa, marigayi Shehu Shagari?

“To hatta ɗakin taro na NOA ɗin ya taɓa zama Zauren Taron Majalisar Zartaswa ta Ƙasa, inda ministoci su ka riƙa yin taron su da Shugaban Ƙasa.

“Idan ka ziyarci ofishin NOA a yau ɗin nan, za ka ga ita kan ta kujerar da marigayi Shugaba Shagari ya riƙa zama a kan ta, lokacin ya na shugaban ƙasa.”

Idris yi kira ga hukumar ta ƙwararrun masu zanen gine-ginen da su ci gaba da tuntuɓa da kuma yin aiki tare da ma’aikatar sa wajen ƙoƙarin sake wayar da kan jama’a, domin ɗabbaƙa kyawawan al’adun mu.

Ya kuma yi tsinkayen cewa jama’a su ne mafi tasirin al’adu da kowace ƙasa za ta yi alfahari da su.

Ya ƙara da cewa idan jama’a su ka rasa kyawawan ɗabi’u da ƙarancin wayewar kai a matsayin su na al’umma, to duk wani ƙoƙarin da ake son a cimma, ba zai yi nasara ba.

Ministan ya yi ƙorafi dangane da  munanan ɗabi’un wasu marasa kishi, waɗanda ba su darajta gine-ginen tarihin ƙasa da sauran ababen da ke haskaka kyakkyawan tarihin mu a matsayin ƙasa, musamman Tutar Nijeriya, Tambarin Nijeriya, fasfo na shaidar ɗan ƙasa da sauran su.

Haka kuma ya ce Shugaba Bola Tinubu ya ɗau himmar kawo kyakkyawan sauyi a zukatan jama’a, dalili kenan ma ya bayar da fifiko da maida hankali kan Shirin Wayar da Kai a matsayin sabon aiki wurjanjan da ya ɗora wa Ma’aikatar Yaɗa Labarai.

Ita kuwa Shugabar Hukumar Masu Zanen Gine-gine ta Ƙasa, Mobolaji Adeniyi, ta nuna cewa a shirye hukumar take wajen haɗa kai da haɗa ƙarfi da Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai domin samun nasara wajen wayar da kan jama’a, musamman a ɓangaren kamfen don nuna wa mutane illolin da ke haddasa rugujewar gine-gine, haɗarin da ke tattare da gini maras inganci ko kayan gini marasa nagarta da sauran hanyoyin da za a taskace gine-gine masu tarihi a ƙasar nan, musamman a Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *