Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga masu ƙirƙira da masu tasiri a shafukan sada zumunta da su rage munanan kalamai kan Nijeriya tare da fifita muradun ƙasar ta hanyar bin ƙa’idojin ɗa’a wajen gudanar da ayyukansu.
Idris ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a 25 ga Oktoba, 2024 a Abuja, yayin bikin Makon Ilimin Yaɗa Labarai da Bayanai na Duniya na Ƙasa na 2024 mai taken “New Digital Frontiers of Information: Media and Information Literacy for Public Interest Information” wanda Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta shirya tare da haɗin gwiwar Cibiyar Ilimin Yaɗa Labarai da Bayanai ta Duniya, Buɗaɗɗiyar Jami’ar Nijeriya.
A wata sanarwa da Rabiu Ibrahim, Mataimaki na Musamman ga Ministan kan Harkokin Yaɗa Labarai ya fitar, Idris ya jaddada muhimmancin daidaita suka da kishin ƙasa, inda ya buƙaci masu ƙirƙira a shafukan sada zumunta da su yi la’akari da muradun ƙasa yayin yaɗa bayanai.
Ya bayyana cewa, “Yana da muhimmanci mu riƙa suka da kuma sanya gwamnati da sauran shugabanni su yi bayani domin aikin kafafen yaɗa labarai kenan…Amma kuma yana da matuƙar muhimmanci a wajen bayar da rahoto, mu fifita muradin ƙasa.”
“Ina sake maimaitawa, ba za mu iya tsammanin girma da kuma samun mutane su zo su zuba jari a ƙasarmu ba yayin da duk abin da muke turawa waje a kowane lokaci ba shi da kyau. Akwai labarai masu kyau da yawa da ke fitowa daga Nijeriya kuma ya zama wajibi mu kasance masu kishin ƙasa yayin da muke bayar da rahoto domin Nijeriya ta kai ga inda take so ta kai na wadata da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi magana a kai,” inji shi.
Ministan ya yi Allah-wadai da yaɗuwar labaran ƙarya a shafukan sada zumunta, inda ya yi gargaɗin cewa, idan ba a daƙile ba, hakan na haifar da barazana ga haɗin kai, zaman lafiya da ci gaban ƙasa.
Ya bayyana cewa, “Duk wanda ke da kwamfutar tafi-da-gidanka ko wayar android zai iya zama mai samar da labarai, wanda zai iya isa ga mutane masu yawa. Sai dai, wannan shimfiɗar wuri na dijital… yana haifar da matsaloli masu muni, musamman tare da yaɗuwar bayanan ƙarya.”
Idris ya yabawa UNESCO bisa ƙoƙarin da take yi na yaƙi da labaran ƙarya a Nijeriya ta hanyar kafa Cibiyar Ilimin Yaɗa Labarai da Bayanai ta Duniya.
Ya sanar da cewa Ma’aikatar Yaɗa Labarai tare da haɗin gwiwar Budaddiyar Jami’ar Nijeriya (NOUN) na ci gaba da mayar da cibiyar ta zama Cibiyar UNESCO ta Rukuni na 2.
Wakilin UNESCO a Nijeriya, Abdourahamane Diallo, ya kuma jaddada muhimmancin shigar da Ilimin Yaɗa Labarai (MIL) cikin tsarin karatun Nijeriya.
Mataimakin Shugaban Buɗaɗɗiyar Jami’ar Nijeriya, Farfesa Olufemi Peters, ya gode wa Ministan bisa goyon bayan da yake bai wa jami’ar wajen ƙarfafa ayyukan Cibiyar Ilimin Yaɗa Labarai da Bayanai ta Duniya da ke cikin jami’ar.