Ministan Yaɗa Labarai ya jaddada muhimmiyar rawar kafafen yaɗa labarai a cikin al’umma

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya sake jaddada muhimmiyar rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen jagorantar al’umma, da inganta fahimtar juna, da kuma bayar da gudunmawa ga gagarumin cigaba.

Idris ya bayyana hakan ne a yayin ƙaddamar da wani shirin talabijin mai taken “Traverse China With Me,” wanda na haɗin gwiwa ne tsakanin Hukumar Talabijin ta Nijeriya (NTA) da kuma China Media Group (CMG) a ranar Alhamis a Cibiyar Al’adun Ƙasar Sin da ke Abuja.

A wajen taron, Idris ya bayyana cewa shirin zai ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin gidajen talabijin na Nijeriya da kafofin watsa labarai na ƙasar Sin, wato Chaina.

Ya ƙara da cewa wannan shiri wani ɓangare ne na ƙoƙarin inganta alaƙa tsakanin al’ummar Nijeriya da Sin ta hanyar musayar al’adu da harshe, ta hanyar amfani da hanyoyin sadarwa na zamani da ake da su a ƙasashen biyu.

Ministan ya yaba wa hukumomin CMG da NTA bisa jajircewar su wajen samar da ingantattun labarai da shirye-shirye masu ma’ana waɗanda ke taimaka wa cigaban ƙasashen biyu.

Ya ce haɗin gwiwar zai yi tasiri mai kyau ga harkokin zamantakewa, cigaban tattalin arziki, da cigaban al’adu.

Idris ya kuma jaddada muhimmancin daidaita rahotanni, musamman wajen bayyana cigaban da aka samu, da kuma samar da shirye-shirye da za su haifar da kyakkyawar fatar samun cigaba a nan gaba.

Ya ce Nijeriya da ke da ɗimbin matasa tana fuskantar ƙalubale da dama da suka haɗa da yaɗa labaran ƙarya da ji-ta-ji-ta waɗanda ke haifar da koma-baya da rashin yarda tsakanin gwamnati da ‘yan ƙasar.

Ya buƙaci kafafen yaɗa labarai na Chaina da su haɗa kai da Nijeriya da sauran takwarorin su na ƙasa da ƙasa don daƙile wannan mummunar ɗabi’a da tabbatar da inganci da aminci a cikin harkar yaɗa labarai.

Bugu da ƙari, ministan ya yi kira ga CMG da ya faɗaɗa kafafen yaɗa labaran sa a Nijeriya ta hanyar haɗawa da wasu harsuna, kamar Hausa, Ibo, Yarbanci, da Pijin.

Ya ce hakan ba kawai zai inganta sadarwa ba, har ma zai samar da guraben aikin yi da horar da ‘yan Nijeriya.

Ita ma Daraktar Sashen Hausa na CMG, Kande Gao, ta yi jawabi a wajen taron, inda ta bayyana alaƙar da ke tsakanin Sin da Nijeriya, tare da yin kira da a ƙara yin hadin gwiwa.

Ta bayyana cewa kamfanin CMG ya himmatu wajen samar da fahimtar juna a tsakanin ƙasashen biyu, kamar yadda ake nunawa a cikin shirye-shirye irin su “Traverse China With Me,” wanda ya samu karɓuwa musamman a yankunan da ake magana da harshen Hausa.

Taron ya samu halartar wakilai daga NTA, gidan Rediyon Nijeriya, Muryar Nijeriya, da Hukumar Kula da Kafofin Yaɗa Labarai a Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *