Ministan Yaɗa Labarai ya jajanta wa Mataimakin Gwamnan Neja kan rasuwar matar sa

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya miƙa saƙon ta’aziyyar sa ga Mataimakin Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Garba Yakubu, da ɗaukacin iyalan sa bisa rasuwar matar sa Hajiya Zainab.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, ministan ya ce, “Ina miƙa saƙon ta’aziyya ta ga Mataimakin Gwamnan Jihar Neja, Mai Girma Alhaji Garba Yakubu, da ɗaukacin iyalan sa bisa rasuwar mai ɗakin sa, Hajiya Zainab.

“Kalamai ba za su iya bayyana baƙin ciki da juyayin da mu ke yi wa Mataimakin Gwamna a wannan lokaci mai matuƙar wahala ba.

“Marigayiya Zainab fitacciyar mace ce wadda kyautatawar ta da sadaukarwar ta su ka taɓa rayuwar mutane da yawa.

“Gudunmawar da ta bayar a Jihar Neja ya bar wa waɗanda su ka yi sa’a da sanin ta tarihin da ba ya kankaruwa.

“Haƙiƙa, rasuwar ta babban rashi ne ba ga Jihar Neja da mata ba, har ma ga ƙasa baki ɗaya.

“A wannan lokaci na makoki, tunanin mu da addu’o’in mu su na tare da Mataimakin Gwamna. Mu na tare da shi, mu na ba da goyon baya da ƙarfin mu yayin da ya ke ji da wannan babban rashi.

“Allah ya jiƙan ta ya kuma bai wa Mataimakin Gwamna da sauran iyalin sa gaba ɗaya ƙwarin gwiwar jure wannan rashi mara misaltuwa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *