Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar da karar shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio kan ikirarin bata suna.
Kamar yadda PM News ta ruwaito, karar wadda aka shigar a babbar kotun birnin tarayya da ke Abuja a ranar 25 ga watan Fabrairun 2025, ta lissafo Akpabio da Mfon Patrick, babban mataimakin shugaban majalisar dattijan a majalisar dokoki, a matsayin wadanda ake kara.
Wannan danbarwa dai ta fara ne bayan an canza wurin da Akpoti-Uduaghan ke zama a majalisar dattijai.
Sanatar ta ki amincewa da canjin da aka yi, inda hakan ya haifar da fito-na-fito da shugaban majalisar dattijan. Al’amarin sai ya ta’azzara, inda Akpoti-Uduaghan ta yi ikirarin Akpabio ya yi kalaman batanci a kan ta wadanda mataimakinsa ya wallafa a kafar sada zumunta ta Facebook.
Kalaman wadanda ake takaddama a kansu da aka wallafa a Facebook na da taken, “is the Local Content Committee of the Senate Natasha’s birthright?” Ya kunshi kalamin da ke yunkurin bayyanawa cewa Akpoti-Uduaghan ta yi imanin cewa kasancewa ‘yar majalisa kawai na nufin “gyara fuskarta ne tare da sa kayan da ake iya ganin jikin mutum zuwa zauren majalisa.”
Lauyan ta, Victor Giwa, ya dage kan cewa kalamin bata suna ne, tonon fada ne kuma rage kima wanda ke bata mutuncin Akpoti-Uduaghan a idon wadanda ta ke tare da su da kasa baki daya.
Natasha na neman a bayyana kalaman da Akpabio ya yi shi da mataimakinsa bata suna ne kuma suna da niyyar haifar da matsala ne daga ‘yan kasa.
‘Yar majalisar dattijan na ma neman kotun da ta hana wanda ake karar da mukarrabansa yin wani kalamin batanci a kan ta a kowacce kafa.
Bayan haka Natasha na neman diyyar naira biliyan 1 saboda bata suna da kuma naira miliyan 300 a matsayin kudin da aka kashe a kotu.
Wannan karar da ta shigar na yin nuni da cigaban zaman dar-dar a tsakanin ta da shugaban majalisar dattijai wanda ya fara sakamakon rashin jituwa biyo bayan canza yanayin zama inda a yanzu kuma ya ta’azzara zuwa shari’a kan bata suna.