Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya sake farfado da matakai a ranar Litinin na kulle tashar talabijin din tauraron dan Adam mai goyon bayan Larabawa ta Al Jazeera a Isra’ila, inda ya bayyana ta bakin kakakin jam’iyyarsa cewa majalisa za ta hadu da yamma domin samar da dokar da ake bukata.
Kamar yadda The New Arab ta ruwaito, bayan nan, Netanyahu “zai dauki mataki ba tare da bata lokaci ba wajen kulle tashar Al Jazeera kamar yadda matakai suka nuna a dokar.” Kamar yadda jawabin jam’iyyar ta Likud ya nuna.
Al Jazeera, wadda ke yin rahotonta a harsunan Larabci da Turanci, na kawo cikakken yadda mummunan yakin Isra’ila a kan Gaza ke kasancewa.
Dama kafin nan Tel Aviv ta yi ikirari yayin yakin na Gaza inda ta ke zargin ‘yan jaridan Al Jazeera da dangantaka da Hamas da sauran kungiyoyin mayaka.