Rundunar sojojin Yemen ta sake harbo jirgin yakin Amurka mara matuki na US MQ-9

Rundunar sojin kasar Yemen ta bayyana cewa ta sake harbo jirgin yaki mara matuki na US MQ-9, kwanaki uku bayan harbo na farko a makon da ya gabata, a matsayin wani bangare na goyon bayan raunana Falasdinawa da kuma hare-haren da Amurka ke jagoranta kan sojojin kasar ta Larabawa, kamar yadda Press TV ta ruwaito.

A cikin wani jawabi a ranar Alhamis, rundunar sojin kasar Yemen ta bayyana cewa makaman tsaron sararin samaniyarsu sun harbo jirgin yakin Amurka mara matuki na MQ-9 Reaper, wanda jirgi ne da aka tsara domin ya kasance mai karko kuma mai nisan iya leko asiri ko sa ido, a sararin samaniyar yammacin al-Hudaydah da ke kasar Yemen.

“Domin nuna goyon bayan raunana mutanen Falasdinawa da kuma nuna goyon bayan yunkurin fafutikarsu, da taimakon Allah Madaukaki, makaman kariyar sararin samaniya na sojojin Yemen sun harbo jirgin yaki mara matuki na Amurka na MQ-9 mai barazana a yayin da ya ke keta alfarmar sararin samaniyar yankin mulki na al-Hudaydah ta hanyar yin amfani da makami masu linzami kirar cikin gida da ake harbawa daga kan-tudu-zuwa-sama.” Kamar yadda Birgediya Janar Yahya Saree, Mai magana da yawun sojin kasar Yemen, ya bayyana a cikin wata hirar gidan talabijin.

Ya bayyana cewa wannan shine jirgi mara matuki karo na biyu da makaman tsaron sararin samaniyar Yemen suka harbo “a cikin awowi 72 kuma na 17 a cikin yakin Alkawarin Nasara da kuma Jihadi Mai Tsarki domin goyon bayan Gaza,” wanda aka fara jim kadan bayan 7 ga watan Oktobar 2023 bayan Isra’ila ta kaddamar da yakin ta na kisan kare dangi a zirin Gaza.

Rundunar sojin a ranar Litinin ta bayyana cewa ta harbo jirgi mara matuki na MQ-9 a tsakiyar yankin Ma’rib.

A ranar Alhamis, rundunar sojin ta Yemen ta kara jaddada aniyarta na kin amincewa da duk wani yunkuri na yin barazana ga kasar Yemen, inda ta jaddada cewa ta hanyar hadin kai da mutanen Yemen za su cigaba da aikin da suke yi na goyon bayan mutanen Gaza, za su cigaba har sai hare-haren Isra’ila a zirin Gaza sun zo karshe kuma ta dakatar da zagayewar da ta yi masa.

A cikin watan da ya gabata shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ya “amince da daukar matakin soji kakkausa” a kan sojin Yemen da kuma akan masu fafutika daga baya kuma ya yi barazanar “karar da su bakidaya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *