SAƘO DAGA MOHAMMED IDRIS, MINISTAN YAƊA LABARAI DA WAYAR DA KAI

A wannan rana ta Lahadi, na wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen ganawa da shugabannin ƙungiyar jama’ar Nijeriya mazauna ƙasar Habasha.

Wannan dama ce da muka samu muka ji matsalolin su tare kuma da ba su tabbacin cewa gwamnati za ta sa hannu a lamarin.

Abu mafi muhimmanci shi ne, sun yi murnar jin irin shirye-shirye daban-daban masu alfanu waɗanda gwamnatin ke aiwatarwa.

Muna addu’ar Allah ya ci gaba ya albarkaci babbar ƙasar mu, Nijeriya, amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *