Dubban jama’a, jagoran harkar Musulunci a Nijeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky, malamai da shugabanni daga kasashe sama da 70 ne suka halarci jana’izar tsohon babban sakataren kungiyar Hezbollah, Sayyid Hassan Nasrallah, a kasar Lebanon.
Kamar yadda kafar watsa labaru ta Daily Struggle ta ruwaito, ofishin jagoran harkar Musulunci a Nijeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky, ya nuna hotunan Shehin malamin tare da sauran mahalartan a filin jirgin sama na kasa-da-kasa da ke Beirut.
Kamar yadda ya ke a rahoton, a ranar Lahadi, 23 ga watan Fabrairun 2025 ne Sheikh Ibraheem Zakzaky ya hadu a sauran miliyoyin mutanen da ke makoki da suka taru a filin wasa na Camille Chamoun Sports City da ke wajen birnin Beirut.
Masu makokin sun ma nuna girmamawarsu ga Hashem Safieddine, magajin Nasrallah, wanda shima wani harin Isra’ila na daban a cikin watan Oktoba ne ya shahadantar da shi.
Tsohon shugaban kungiyar Hezbollah, Nasrallah, ana kallonsa a matsayin daya daga cikin masu fada a ji a Yammacin Asiya da kuma a matakin duniya.
Awanni kafin fara jana’izar, Isra’ila ta kaddamar da hare-hare ta sama a kudancin Lebanon.
A yayin jana’izar, sakataren kungiyar fafutika ta Hezbollah da ke Lebanon, Naim Kassem, ya yi yabo ga marigayi Sayyid Hassan Nasrallah sakamakon gudunmuwarsa ga fafutikar al’ummar Falasdinawa. Ya sha alwashin cewa Hezbollah za ta cigaba da dagewa ta kuma cigaba a kan turbar Nasrallah.
“Taimakon Nasrallah ba karami ba ne ga fafutikar Falasdinawa. Za mu yi riko da amanar kuma mu cigaba a kan turbarsa.” Kamar yadda Sheikh Kassem ya bayyana.
Nasrallah ya yi shahada ne biyo bayan hare-haren Isra’ila ta sama a kudancin Beirut a ranar 27 ga watan Satunbar 2024, bayan kwashe tsawon mako daya na harin boma-bomai kan kudanci zuwa babban birnin kasar ta Lebanon.
Safieddine shima ya yi shahada ne sakamakon harin Isra’ila a ranar 3 ga watan Oktobar 2024.
Kungiyar Hezbollah ta dage taron jana’iza ga duka shugabannin biyu sakamakon tsoron yiwuwar harin Isra’ila a kan tarukan.