Shirin Rage Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Tarayya za ta fara biyan sabon tsarin albashi daga Afrilu 2024 – Minista

Shugaban kasa, Tinubu 

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta fara biyan ma’aikata da sabon tsarin ƙarin albashi daga ran 1 ga Afrilu, 2024.
Ministan Yaɗa da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, a Abuja, lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai.
Idris ya ce gwamnatin tarayya za ta daina biyan naira 30,000 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi daga ƙarshen watan 2024.
Bayan wani nazari mai zurfi da majiɓinta kula da harkokin kuɗaɗen gwamnatin tarayya suka yi, an bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ɗin za ta kashe har naira tiriliyan 24.66 a shekarun 2024, 2025 da 2026 wajen biyan albashi.
Bayan Shugaba Bola Tinubu ya cire tallafin fetur a ran 29 ga Mayu, 2023, sai Gwamnatin Tarayya ta bijiro da ƙarin naira 35,000 kan gundarin albashin kowane ma’aikacin, a matsayin tallafin rage raɗaɗin tsadar rayuwa na wani taƙaitaccen lokacin watanni shida.
To sai dai kuma a lokacin, ƙungiyar ƙwadago ta tayar da ƙayar baya cewa tallafin na toliyar naira 35,000 kan albashin ma’aikata, lasa zuma a baki ne, tunda ba na dindindin ba ne.
Maimakon haka, ‘yan ƙwadago sun karci ƙasa tare da jajircewa lallai sai dai a yi ƙarin albashi ɗungurugum a 2024.
Bayan shafe watanni ana je-ka-ka-dawon tattaunawa, wakilan Gwamnatin Tarayya ta da na Majalisar Tarayya Al’amurran Ma’aikatan Tarayya (NPCNC), sun cimma amincewa dangane da batun naira 30,000 mafi ƙanƙantar albashi daga ran 18 ga Oktoba, 2019.
Sai dai kuma a ranar Alhamis ƙungiyoyin ƙwadago sun bayyana cewa sun fara tattaunawa da Gwamnatin Tarayya, tare da jaddada cewa dokar biyan haƙƙin leburan Gwamnatin Tarayya ta shar’anta cewa duk bayan shekaru biyar a riƙa yi wa ma’aikata ƙarin albashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *