A ƙoƙarin da ma’aikatar sa ke yi na fara shirin wayar da kan jama’a, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya kafa kwamitin da zai tsara daftarin cusa wa ‘yan Najeriya ɗa’a, kishin ƙasa da kuma kyawawan ɗabi’u.
Daftarin Ɗa’a, Kishin Ƙasa da Kyawawan Ɗabi’u dai ya ƙunshi tamkar wasu shikashikai ne da ɗan Nijeriya zai ƙudurta amfani da su a zuciya da kuma aikace, waɗanda suka ƙunshi halaye nagari.
Shugaba Bola Tinubu ne zai ƙaddamar da shirin a farko-farkon 2024.
Zai ƙunshi Ƙudirorin Alƙawarin Zama Ɗan Ƙasa Nagari, wanda ke ɗauke da shikashikai bakwai kowane.
Gwamnatin Tarayya ta ƙudiri aniyar cusa wannan shirin ɗabbaƙa kishin ƙasa da kyawawan ɗabi’u a cikin manhajar karatu da kuma mu’amalar yau da kullum.
Gwamnatin Bola Tinubu na so ta ƙarfafa kyakkyawan tsarin zamantakewar ‘yan Nijeriya, a matsayin su na ‘yan ƙasa ɗaya amma kuma mabambantan ƙabilu da al’adu.
Kan haka ne ake ƙoƙarin shata tsarin wanda zai ƙara ƙarfafa ƙasar ta zama mai al’umma ɗaya, kuma mai dunƙulalliyar kyakkyawar mu’amala, ɗa’a da kishin ƙasa.
Cikin sanarwar da Mataimakin Daraktan Yaɗa Labarai na Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Suleiman Haruna ya sa wa hannu kuma ya fitar a ranar Laraba, ya ce Daraktar Wayar da Kai da Cusa Kyawawan Ɗabi’u (OBM) a Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA) ce, Theresa Nnalue za ta tafiyar da ayyukan kwamitin.
Wannan kwamiti dai ya ƙunshi mutum 9, ƙarƙashin Dakta Muhammad Auwal Haruna, a matsayin shugaba.