Shugaban kasar Brazil ya ce ba a zabi Trump domin ya ‘mulki duniya’ ba

Daga Abubakar Musa

Shugaban kasar Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva, ya ce shugaban kasar Amurka Donald Trump an zabe shi ne domin ya mulki Amurka, ba ‘domin ya mulki duniya’ ba.

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, Lula ya bayyana cewa, “Ina girmama zaben shugaban kasa Trump, wanda mutanen Amurka suka zaba domin ya mulki Amurka” amma “ba an zabe shi ba ne domin ya mulki duniya.”

Shugaban na Amurka ya kamata ya girmama dangantakar “damakaradiyya da wayewar kai” da sauran kasashen duniya, kamar yadda Lula ya nuna inda ya ke nufin niyyar Trump na canzawa Falasdinawan da ke zirin Gaza matsugunni.

Trump dai a yayin wani taron manema labaru a ranar Talata ne ya bayyana cewa Amurka za ta karbe ikon mallakar zirin Gaza tare da ginawa bayan Falasdinawa sun koma wani wajen.

Shugaban na Brazil ya ma soki Trump da nuna kan sa a matsayin wani “alami na damakaradiyya kuma mai ‘sanya ido’ na duniya.”

Ya ma bayyana kalaman Trump na mamaye wasu kasashe da yankuna a matsayin “tonon fada.” Kamar yadda ya ke a rahoton na Vanguard.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *