Sojan saman Amurka ya mutu bayan ya sa wa kan sa wuta a kofar ofishin jakadanci Isra’ila

Wani sojan saman Amurka ya mutu bayan ya sawa kan sa wuta a ranar Lahadi a kofar ofishin jakadancin Isra’ila da ke Washington, D.C.

Kamar yadda kafar watsa labaru ta The New Arab ta ruwaito, wani bidiyo da aka wallafa a kafar sadarwa ya nuna mutumin yana fada da karfi “Free Palestine” yayin da ya ke ci da wuta yayin al’amarin wanda ya dauki kimanin minti daya kafin jami’an tsaro su kashe wutar.

Mutumin, wanda aka bayyana sunansa da Aaron Bushnell, mai shekaru 25, daga San Antonio, an gan shi a cikin kakin soja kuma ya bayyana kansa da “mamba mai aiki ga sojin sama na Amurka.”

Kakakin rundunar sojin saman Amurka, Ann Stefanek, ta tabbatar ta hanyar sakon Imel a ranar Lahadi da yamma cewa “Sojan sama da a yanzu haka yana aiki al’amarin na yau ya shafa.”

Sahen ‘yan sandan yanki (MPD) sun bayyana a cikin wani jawabi a ranar Litinin cewa bayan wadanda suka zo na farko wurin da al’amarin ya faru mutumin “jami’an DC Fire da EMS sun tafi da shi asibitin yanki inda daga bisani ya rasu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *