Rundunar sojin Isra’ila ta hana daruruwan masu gudanar da ibada kaiwa ga masallacin Al-Aksa da ke Jerusalem da aka mamaye domin yin sallar Juma’a ta biyu a cikin wata mai tsarki na Ramadana, kamar yadda kamfanin dillancin labaru na WAFA ya ruwaito.
Kamar yadda ya ke a cikin rahoton The New Arab, shaidun gani da ido sun ruwaito yawaitar sojoji a shingayen da ke Kalandia, arewacin Jerusalem, Al-Zaytouna, gabashin Jerusalem da kuma Bethlehem daga kudanci.
Kamar yadda kafar ta ruwaito, sojojin Isra’ila suna hana kaiwa ga masallacin Al-Aksa a cikin wata mai tsarki, inda suke hana shiga tare da sa shingayen karfe, a yayin da kuma mazauna ‘yan kama wuri zauna na Isra’ila ke afkawa harabar.