Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya koka kan yiwuwar kama shi da tsare shi.
Kamar yadda Daily Post ta ruwaito, El-Rufai ya bayyana cewa ya ji rade-radin yiwuwar kama shi amma sai ya bayyana cewa ba ya da niyyar zuwa wani wuri.
Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya ke bayar da amsa ga wani babban mai goyon bayansa, Imran Wakili, dangane da ikirarin shirin kamawa da tsare shi.
El-Rufai, wanda a yanzu haka yana kasar Misra, ya ce ya shirya ya dawo Nijeriya kafin 20 ga watan Fabrairu.
“Zan dauki lokaci sosai a Nijeriya fiye da lokacin baya.” Kamar yadda El-Rufai ya rubuta.
“Sun tura sakonnin tsoratarwa da barazana irin wannan ta hanyar abokaina, iyali da abokanan siyasa domin suna so domin kashin kai na in tafi zuwa wani wuri.
“A yanzu na tsayar da dukkanin tsarin karatu da koyon yare na. Shiru ba shine abin yi ba kuma. Rashin yin wani abu ba zai taba zama zabi ba.
“Kamawa, tsarewa da horo ga wadanda ake ganin abokan gaba ne na siyasa ba sabon abu bane a harkokin rayuwar dan Adam. An kama ni an tsare ni sau uku a baya domin na bayyana ra’ayi na a kan gwamnatocin baya.
“Komai na wucewa bayan kamu ko tsarewa ko horo, kuma rayuwar siyasa ta cigaba. Ita kuwa mutuwa, sai lokacin da Allah Ya nufa, kuma tana wuyan kowanne dan Adam.
“Ga wadanda ba su yin barci sosai a duk lokacin da na ke a Nijeriya, ku sani na yi niyyar dawowa lokacin kaddamar da tarihin da (tsohon) shugaban kasa IBB (ya rubuta) in shaa Allah wanda za a yi ranar 20 ga watan Fabrairun 2025.
“Ba mu dogara da kowa ba sai Allah. Ba ma jin tsoron kowa sai Allah. A kodayaushe muna fatar samun abinda ya fi kyau amma muna shiryawa akasin haka.”
El-Rufai a yanzu haka yana rigima ne da magoya bayan shugaban kasa Bola Tinubu da mambobin jam’iyyar APC.
Ba dadewa ya zargi APC da cewa ta rasa damakaradiyyar cikin gida, inda ya kawo hujjar cewa bangarorin jam’iyyar ba su hadu ba tsawon shekaru biyu da suka gabata.