Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa za ta yi rabon tallafin kayan abincin da Gwamnatin Tarayya ta ba jihar.
Cikin sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya yi wa taron manema labarai a ranar yammacin Lahadi, ya ce Jihar Kano ta karɓi lodin mota 100 na ƙaramin buhun shinkafa, na dawa mota 44, na gero 14, masara 41 a matsayin kayan tallafi daga gwamnatin tarayya, waɗanda ya ce za a raba a cikin makon nan.
Ya ce za a yi rabon kayan abincin a dukkan mazaɓu 484 da ke cikin ƙananan hukumomin Kano 44.
A ranar Talata ne kuma Gwamna Yusuf ya wakilta Mataimakin Gwamna Aminu Abdulsalam Gwarzo aikin rabon kayan tallafin abinci da Cibiyar Agaji da Jinƙai ta Sarki Salman da ke Saudiyya ta raba wa gidaje 2056 a cikin rukunin ƙananan hukumomi 8 da ke cikin birni da kewaye.
An dai fara rabon abincin a Gidan Hatsi da ke kan Titin Maganda da ke cikin Ƙaramar Hukumar Nassarawa, cikin birnin Kano.
Gwarzo ya ce wannan ne karo da uku da Cibiyar Agaji ta Sarki Salman ke bayar da tallafin abinci a Jihar Kano.