Ashafa Murnai Barkiya
A ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardoso, CBN ya gudanar da taron Kwamitin Gudanarwa na 35 na manyan bankunan duniya guda takwas, wato International Islamic Liquidity Management Corporation (IILM) a karon farko a Nijeriya, a Hedikwatar CBN da ke Abuja.
Wannan taron dai ya yi daidai da wa’adin Gwamna Cardoso a matsayin Shugaban Kwamitin Gudanarwa na IILM, wanda tabbas ke nuna ƙaruwar tasirin Nijeriya a fannin hadahadar bisa tsarin kuɗin Islama na duniya da kuma jajircewar ta wajen ƙarfafa kasuwancin kuɗin da ba su da ruwa.
Shugabannin manyan bankuna daga Indonesiya, Kuwait, Malesiya, Mauritius, Nijeriya, Qatar, Turkiyya, UAE da ICD ne suka hallara domin tantance nasarorin da suka samu a cikin shekarar 2025 da kuma saita muhimman abubuwan da za a mayar da hankali a kansu cikin tsarin kula da kuɗaɗe na duniya.
A lokacin shugabancin Nijeriya na shekarar 2025, Kwamitin Gudanarwa na IILM ya samu gagarumin ci gaba, wanda ya haɗa da ƙarin fitar da takardun sakamako na SUKUK, faɗaɗa yawan masu zuba jari, da ƙarfafa kayan aikin likwiditi ga cibiyoyin kuɗi na Islama.
CBN ya kuma gudanar da taron ƙwarewa kan Gudanar da Tsarin samar da kuɗaɗe ta hanyar SUKUK, na Islama ga sashen bankunan da ba su da ruwa a Nljeriya, wanda ya ƙara inganta ƙwarewar fasaha da bunƙasa kasuwa.
Nijeriya ta ƙara tabbatar da jajircewarta ga tsarin kuɗi na duniya na game-gari, tare da karfafa amincewar masu zuba jari a sashen kuɗin da ba shi da ruwa da ke bunkasa, ta hanyar gudanar da wannan muhimmin taro.
IILM dai wani kwamiti ne na Manyan Bankunan ƙasashe takwas da kuma wata babbar ƙungiya ta duniya, domin samar da kuɗaɗe a bisa tsarin da Shari’ar Muslunci ta tanadar, wato SUKUK.
