Tasirin Shaikh Ibraheem Zakzaky A kan Fahimta Da Girmama Sayyida Zahara (AS)

Babban tasirin Shaikh Ibraheem Zakzaky wajen fahimtar Sayyida Zahara (AS) da girmama Sayyida Zahara (AS) a Nijeriya, tafiya ce mai kawo sauyi wacce ta wuce iyakokin addini. Shahararren Malamin addinin Musuluncin nan na Najeriya kuma Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya ya taka rawar gani wajen kara fahimtar Sayyida Zahara, diyar Annabi Muhammad (SAW) a tsakanin al’ummar Musulmin Najeriya.

Tushen koyarwar Shaikh Zakzaky ya ta’allaka ne a kan sadaukar da kai wajen bunkasa ilimi da dabi’u na Musulunci, kuma ba a tantama a kan muhimmancin Sayyida Zahara a tarihin Musulunci. Ta hanyar dimbin laccoci da wa’azi da rubuce-rubucensa, Shaikh Zakzaky ya yi kokarin haskaka rayuwa da kyawawan halaye da sadaukarwar Sayyida Zahara, tare da samawa mabiyan sa cikakkiyar fahimtar rawar da ta taka a farkon Musulunci.

Daya daga cikin muhimman abubuwan da Shaikh Zakzaky yake koyarwa, shi ne yadda ya ba da fifiko a kan kyawawan dabi’u na Sayyida Zahara a matsayin alama ta takawa, tsayin daka, da ibada. Ta hanyar zurfafa bincike a cikin bayanan tarihi da nassosin addini, ya fayyace jajircewarta marar kakkautawa ga ka’idojin adalci, tausayi, da tsayin daka wajen fuskantar wahala. Wannan labari ba wai yana karfafa alaka ta ruhi na mabiya da Sayyida Zahara kadai ba, har ma ya zama tushen abin zaburarwa don kewaya kalubale na wannan zamani tare da manufa da adalci.

Bayan haka, tasirin Shaikh Zakzaky ya wuce fagen bahasin addini zuwa ga zamantakewa ta yau da kullum. Harkar Musulunci a Najeriya karkashin jagorancinsa ta taka rawar gani wajen gudanar da ayyukan jin kai da ci gaban al’umma daban-daban. Ta hanyar koyi da darajojin da Sayyida Zahara ke nunawa, kamar karamci da kuma kula da jin dadin sauran jama’a, Shaikh Zakzaky ya karfafa gwiwar mabiyansa da su rika bayar da gudummawa sosai wajen ci gaban al’umma, ta yadda za a rika daukar nauyi da kuma cudanya da al’umma.

Tarurrukan Maulidin Sayyida Zahara da juyayin shahadarta a kowace shekara, ya zama wani gagarumin biki a cikin Harkar Musulunci a Nijeriya. Shaikh Zakzaky yana amfani da wannan lokaci wajen zurfafa bincike a cikin rayuwa da tarihin Sayyida Zahara, tare da samar da yanayi na tunani na ruhi da makoki a tare. Tarukan kan zama wani abin da zai hada kan al’umma, wajen karramawa da kuma samun kwarin gwiwa daga koyarwa da sadaukarwar Sayyida Zahara.

Duk da kalubalen da Shaikh Zakzaky yake fuskanta na yada ilimi a kan Sayyida Zahara har yanzu yana nan daram. Kokarin nasa ba wai kawai ya ba da gudummawa wajen kara fahimtar tarihi da dabi’u na Musulunci ba, har ma ya samar da fahimtar hadin kai da sanin ya kamata a tsakanin Musulmin Nijeriya.

A karshe, Tasirin Shaikh Ibraheem Zakzaky wajen fahimtar Sayyida Zahara da girmama Sayyida Zahara ya wuce koyarwar addini kawai. Ya ƙunshi cikakken tsari wanda ke haɗa wayewar ruhaniya tare da zamantakewa. A kokarinsa na sadaukar da kai, Shaikh Zakzaky ya kafa harsashin gina al’ummar da ba wai kawai ta girmama Sayyida Zahara ba ne, har ma da kokarin sanya kyawawan dabi’unta a cikin rayuwarsu ta yau da kullum, wanda hakan ya haifar da tasiri mai dorewa a fagen addini da zamantakewar Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *