Tinubu ya naɗa Mohammed Idris cikin kwamitin yi wa Shirin Inganta Rayuwar Marasa Galihu garambawul

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a

Shugaba Bola Tinubu ya kafa kwamitin ministoci shida wanda zai yi wa Shirin Inganta Rayuwar Marasa Galihu (NSIP) garambawul.

Kafa kwamitin ya biyo bayan dakatar da shirin da Tinubu ya yi, mako ɗaya bayan dakatar da Ministar Harkokin Agaji da Jinƙai, Dakta Betta Edu.

Shugaban Ƙasar ya dakatar da Edu ne bayan sauke jagorar raba Tattalin Marasa Galihu, Hajiya Halima Shehu.

An zargi Edu da karkatar da naira miliyan 585.2 cikin asusun bankin wata ma’aikaciyar gwamnati.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labarai na Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Asabar, ya ce kwamitin da Tinubu ya naɗa ya ƙunshi ministoci shida ƙarƙashin Ministan Harkokin Kuɗaɗe, kuma Ministan Kula da Tattalin Arziki, Mista Wale Edun.

Sauran sun haɗa da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris; Ministan Lafiya, Dakta Ali Pate, da Ministan Kasafi Da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Alhaji Abubakar Bagudu.

Akwai kuma Ministan Sadarwa da Ƙaramin Ministan Harkokin Matasa.

Ngelele ya bayyana nauyin da aka ɗora wa kwamitin, inda ya ce: “An ɗora wa Kwamitin Musamman na Shugaban Ƙasa nauyin gaggauta fara bin diddigin kashe kuɗaɗen Shirin Inganta Rayuwar Marasa Galihu da kuma duba tsare-tsare da ƙa’idojin shirin baki ɗaya. 

“Za su yi haka ne domin sake wa shirin fasalin tsare-tsaren raba kuɗaɗe a ayyukan tallafin marasa galihu, shirin ciyar da ‘yan makaranta da tallafa wa masu ƙananan sana’o’i. Sai kuma Shirin N-Power da na tallafin kuɗaɗe ga marasa galihu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *