Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya kafa kwamitoci biyu na binciken sayar da kadarorin gwamnatin jiha, rigingimun siyasa da kuma binciken ɓacewar wasu mutane da aka daina jin ɗuriyar su daga 2015 zuwa 2023.
Da ya ke ƙaddamar da kwamitocin a ranar Alhamis, Gwamna Abba ya sha alwashin sai an hukunta duk wani da aka samu da hannu wajen aikata laifi ko laifukan da za a binciko.
Cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna, Sanusi Bature ya fitar a ranar Alhamis, gwamnan ya tunatar wa kwamitin binciken salwantar Kadarorin cewa binciken wannan badaƙala na ɗaya daga cikin alƙawurran da ya ɗauka a ranar da aka rantsar da shi.
“Hargitsin siyasa na daga cikin abin da ke kawo koma-baya a dimokraɗiyya duk duniya. Kuma shi ne ke kai ga asarar rayuka da dukiyoyi da rashin amannar da talakawa ke yi wa masu mulki.”
“Akwai munanan rikice-rikicen da suka haifar da rasa rayuka musamman a 2023, waɗanda ba za a ba su baya a manta da su ko a binne su ba. Za a binciko su domin tabbatar da irin haka ko makamancin hakan bai sake faruwa ba.”
Kwamiti na farko ya na ƙarƙashin Mai Shari’a Zuwaira Yusuf, shi ne kuma zai binciki rigingimun siyasa na 2015 zuwa 2023.
“Shi wannan kwamitin muna so ya binciko irin yadda aka ƙulla rikicin, sannan a bankaɗo waɗanda duk ke da hannu ko ma su wane, domin a hukunta su. Kwamitin zai bankaɗo musabbabin tashin rikice-rikicen a 2015, 2019 da 2023.”
Shi kuma kwamiti na biyu da ke ƙarƙashin Mai Shari’a Faruk Lawan, shi ne wanda Gwamna Abba ya ɗora wa nauyin bibiya da bankaɗo yadda aka sayar da kadarorin gwamnatin Kano.
Abba ya hori kwamitin da sauran ɗaukacin mambobin sa kada su saurara ko jan-ƙafa wajen gano yawan kadarorin gwamnati da aka sayar, musamman lokacin gwamnatin da ya gada.
Ya ce a gano yawan kadarorin na gwamnatin Kano da aka salwantar a ciki da wajen jihar Kano.
Sai dai Gwamna Abba ya ce wannan gagarimin aikin da ya ɗauko ba siyasa ba ce, kuma ba wasu ɗaiɗaikun mutane ya ke harin kamawa ba.
Ya ce nauyi ne da alar Jihar Kano ta ɗora masa, shi kuma zai cika alƙawarin saukewa.
Gwamnan ya ba kwamitin watanni uku ya kammala bincike tare da miƙa masa rahoton sakamakon bincike.