Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta fito da wasu tsare-tsare waɗanda za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasar nan tare da samar da aikin yi.
Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Dakta Doris Uzoka-Anite, ita ce ta bayyana haka a wurin wani taro na musamman da ‘yan jarida wanda Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, a ƙarƙashin minista Alhaji Mohammed Idris, ta shirya a ranar Juma’a a Cibiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa da ke Abuja.
Taron shi ne na biyu a ci gaba da jagorantar ministoci da Idris ke yi domin su riƙa bayyana wa manema labarai irin ci gaban da suka samar a watanni shida da su ka yi, sai kuma bayyana masu irin alƙiblar da ake fuskanta nan gaba.
Tun da farko, Idris ya buɗe taron da jawabi inda ya ce: “Mun taru a nan domin gina ginshiƙin yarda, amanna a tsakanin mu da ‘yan jarida, ta yadda za mu tabbatar cewa ana sanar wa jama’a abin da muke aiwatarwa.
“Wannan taro ya ba ku damar ku gana kai-tsaye da manyan jami’an gwamnati, ku yi mana tambayoyin da suka cancanta da waɗanda suka shige wa jama’a a duhu.”
Ministan ya jaddada ƙoƙarin da ma’aikatar sa ke yi wajen yin komai a fili ba tare da ƙumbiya-ƙumbiya ba.
Ya nanata damar samun bayanai da manema labarai ɗin ke da ita, tare da bayyana muhimmiyar rawar da ‘yan jarida ke takawa wajen isar da saƙonni ga jama’a.
Haka kuma ya ƙara nuna ƙoƙarin tabbatar da yaɗa labarai a kusa da nesa, ta hanyar da aka saba da kuma sabbin hanyoyin na’urorin zamani masu kai saƙonni nesa, nan take.
Ya ce: “Mun haƙƙaƙe cewa mu na bisa turbar cimma ƙudirin shirin Shugaban Ƙasa na Fata Nagari. Za mu ci gaba da sanar da ku duk wani cigaba da ake samu a duk lokacin da mu ka matsa gaba kaɗan, mu ka ɗan yada zango.”
Yayin da ta ke nata jawabin ga manema labaran, Dakta Doris Uzoka-Anite ta zayyana shirye-shiryen bunƙasa tattalin arzikin da ta bijiro da su, waɗanda ta ce har samar da ɗimbin ayyukan yi ga ɗimbin ‘yan Nijeriya za su yi.
Ta ce dukkan waɗannan shirye-shirye sun ta’allaƙa ne bisa turbar shikashikai takwas na Shirin Shugaban Ƙasa na Fata Nagari, wanda a Turance ake kira ‘Renewed Hope,’ waɗanda su ka haɗa da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa, samar da ayyukan yi, samar da jari, samar da yanayin gudanar da kasuwanci mai yalwa, rage fatara da talauci.
Ministar ta ce ma’aikatar ta na nan ta na tattauna yadda Nijeriya za ta samu damar cin gajiyar tsarin gudanar da cinikayya a sauƙaƙe tsakanin ƙasashen Afrika, wato AFCFTA.
Ta ce gudanar da wannan kasuwanci kai-tsaye ba tare da tarnaƙi ba zai faɗaɗa kasuwanci tsakanin ƙasashen Afrika, kuma zai ƙara ba da damar shigowar masu zuba jari.
Ta ce a taron baya-bayan nan na 13 na Ministocin Kasuwanci da Cinikayya na AFCFTA, an jaddada matsayin da Nijeriya ke da shi wajen bunƙasar kasuwanci ta hanyar fasahar zamani, sai kuma ƙoƙarin da ƙasar ke yi wajen daƙile haramtaccen ciniki ta hanyar amfani da jiragen ruwa.
Uzoka-Anite ta ce, “Ma’aikatar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari na taka muhimmiyar rawa wajen ƙoƙarin sauke nauyi ko tabbatar da nasarar shikashikan gwamnatin Shugaba Tinubu.”
Daga cikin waɗanda su ka halarci taron akwai Mashawarcin Shugaban Ƙasa na Musamman kan Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, da Babbar Sakatare a Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Dakta Ngozi Onwudike, da shugabannin hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatun biyu.