Yadda ‘yan ta’adda suka sace dalibai kusan 300 a Kaduna

Dalibai da malamai kusan 300 aka bayyana ‘yan bindiga wadanda ake zargin ‘yan ta’adda ne da a karkara aka fi sani da ‘yan fashi sun yi garkuwa da su, a kauyen Kuriga, karamar hukumar Chikun da ke jihar Kaduna.

Kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito, wadanda abin ya shafa da suka hada da shugaban makarantar da wasu ma’aikata, an yi garkuwa da su ne a safiyar ranar Alhamis a makarantar LGEA Kuriga.

Yayin da yake tabbatar da aukuwar al’amarin, tsohon sanatan jihar Kaduna, Shehu Sani, a cikin wani rubutu a shafinsa na X a ranar Alhamis ya bayyana cewa al’amarin ya faru ne a kauyen da aka kashe wani shugaban makarantar sakandare, Idris Sufyan, matarsa kuma aka sace ta fiye da wata daya.

“Abin tashin hankali ne jin cewa ba dadewa an yi garkuwa da dalubai 232 a kauyen Kuriga, karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.

“Kauye ne inda aka kashe shugaban makarantar sakandare, Idris Sufyan, matar sa kuma aka yi garkuwa da ita fiye da wata daya. Sai dai, ina cike da fatan za su samu ‘yanci,” kamar yadda ya bayyana.

Karama da babbar sakandiren sun dawo garin Kuriga ne ‘yan shekaru kadan baya saboda damuwar tsaro, inda suka bar tsohon ginin makarantar su wanda yake a bayan gari.

Sai dai, Mansir Hassan (ASP), jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ya tabbatar da al’amarin ga Sahara Reporters inda ya bayyana cewa yawan wadanda abin ya shafa har yanzu ba a tabbatar da shi ba.

“Gaskiya ne, an yi garkuwa da mutane, a yanzu haka mun kara yawan jami’an tsaro a daji domin ceto wadanda abin ya shafa.”

“Duka jami’an tsaro a jihar, ‘yan sanda, sojoji, ‘yan bijilanti baki daya sun hada karfi, kuma a yanzu haka suna cikin dajin suna aiki tukuru domin ceto wadanda abin ya shafa,” kamar yadda ya kara da cewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *