Firaministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya yi gargadin yaki zai dawo a Gaza in Hamas ba ta saki ‘yan HKI da ta yi garkuwa da su ba zuwa ranar Asabar.
Kamar yadda Nigerian Tribune ta ruwaito, kalaman na shi na zuwa ne bayan Hamas ta bayyana a ranar Litinin cewa ba za ta saki wadanda ta yi garkuwa da su mutum uku ‘yan HKI ba kamar yadda aka shirya, inda ta bayar da dalilan karya yarjejeniyar tsagaita wuta da HKI din ke yi.
Hamas ta yi ikirarin cewa HKI ta karya ka’idar yarjejeniyar tsagaita wutar ta tsawon makonni uku, ciki har da hana shigar kayan agaji – ikirarin wanda HKI din ba ta amince da shi ba
Kamar yadda BBC ta bayyana, Netanyahu ya tabbatar da shirin HKI na dawo da cigaba da yakin, inda ya bayyana cewa sojojin HKI “za su dawo da yaki gadan-gadan har sai a karshe an yi nasara kan Hamas.”
Tun da farko, shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana shakku kan ko Hamas za ta iya yin hakan kafin cikar wa’adin, inda ya ce ya yi imanin kungiyar ba za ta amince ba.
A ranar Litinin, ya nemi HKI da ta kyale “Duk abubuwa su lalace” in Hamas ta ki sakin sauran wadanda ta yi garkuwa da su.
Yayin da ya ke jawabi dangane da kalaman na Trump bayan ganawarsa ta tsawon awanni hudu da majalisar tsaron HKI a ranar Talata, Netanyahu a cikin wani bidiyo ya ce ya yi “maraba da bukatar ta Trump.”
“Idan Hamas ba ta dawo da mutanenmu da ta yi garkuwa da su ba zuwa yammacin ranar Asabar, yarjejeniyar tsagaita wutar za ta kawo karshe kuma IDF (rundunar sojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila) za ta dawo da cigaba da yaki har sai an yi galaba a kan Hamas daga karshe.” Kamar yadda Firaministan Haramtacciyar Kasar ya bayyana a wani bangaren jawabin da ya gabatar.