Yan Houthi sun shirya domin haramta duk wani jirgin ruwa da ya shafi Isra’ila, wanda yake mallakin Amurka, Ingila

Kungiyar ‘yan Houthi da ke Yemen sun sanar da haramtawa jiragen ruwan da suka shafi Isra’ila da kuma wadanda suke mallakin Amurka da Ingila wucewa ta tekun Red Sea.

Kamar yadda The New Arab ta ruwaito, duk wani jirgin ruwan da ke tafiya dauke da tutar Birtaniya ko Amurka za a haramta masa wucewa, kamar yadda kamfanin dillancin labaru na Reuters ya ruwaito.

A wani bangaren guda, kafar ta The New Arab ta ruwaito cewa kungiyar Hezbollah ta bayyana cewa ta kai hari a wani waje da ke dauke da sojojin Isra’ila a Kfar Yuval, da ke arewacin Isra’ila.

Kamar yadda ta ruwaito, Hezbollah ta kara da cewa harin an yi shi ne sakamakon hare-haren Isra’ila a kan gidajen fararen hula da kuma kauyuka a kudancin Gaza – da kuma nuna goyon baya ga Falasdinawa da ke Gaza.

Kafofin watsa labarun Isra’ila, yayin da suke nakaltowa daga “Upper Galiliee Regional Council”, sun ma ruwaito cewa wani makami mai linzami da aka harbo daga Lebanon ya lalata gida.

Kafar watsa labaru ta Jerusalem Post ita ma ta ruwaito cewa wani makami mai linzami ya fado a wani fili a Kiryat Shmona.

Ba a ruwaito wasu sun samu raunuka ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *