A yayin da ake sa ido kan shari’ar nan da ake yi da wani kamfanin hada-hadar kuɗaɗen kirifto mai suna Binance, da wani daga cikin jagororin kamfanin wanda ya karya doka wajen hadahadar, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce za a bi dukkan matakan doka da oda da aka saba da su a Nijeriya a shari’ar.
A cikin wata sanarwa da Rabi’u Ibrahim, mataimakin sa na musamman kan yaɗa labarai ya fitar a ranar Laraba, Idris ya bayyana cewa ana bin dukkan ƙa’idojin doka wajen gudanar da shari’ar.
Ya ce, “A kowace gaba, ana bin doka da oda, kuma masu gabatar da ƙara su na da yakinin samun nasara a shari’ar, ganin irin ƙwararan shaidu da hujjoji da aka tattara.
“Binance zai sami damar kare kan sa a kotu game da waɗannan manyan tuhume-tuhume na almundahanar kuɗi da ya tafka a Jamhuriyyar Tarayyar Nijeriya. Za a ci gaba da sauraren ƙarar a ranar 20 ga Yuni, 2024.”
Idris ya bayyana cewa an bai wa Binance, wanda ke kare kan sa a shari’ar, duk wata dama da duk wata kulawar da ta dace, sakamakon samun kula ta ofishin jakadanci da diflomasiyya da aka saba da su, ya ƙara da cewa alƙalin da ke shari’ar ya bayar da gamsasshen bayanin cewa an hana beli ne ga jami’in kamfanin saboda akwai yiwuwar ya tsere, ganin cewa wanda ake tuhumar su tare ya gudu, kuma yanzu haka ‘Yan Sandan Ƙasa da Ƙasa (Interpol) suna neman sa.
Idan za a iya tunawa dai, Binance ya samu ribar sama da dala biliyan 20 a Nijeriya a cikin 2023 kadai, wanda wannan kuɗin ya zarce kasafin kuɗin da gwamnatin tarayya ta yi wa harkokin kiwon lafiya da ilimi, kuma ya haifar da badaƙalar da ta faru a kasuwar canji tare da matsalar tsadar rayuwa.
Bugu da ƙari, Binance ba shi da rajista a Nijeriya kuma bai taɓa biyan haraji ba, sannan ya yi ta harkokin sa ba tare da an sa masa ido ba, kawai ya na cin karen sa ba babbaka da bin ƙa’idojin hana aikata laifukan kuɗi.
Idris ya ce abu ne mai muhimmanci a kalli Binance a matsayin wani kamfani wanda jami’an sa aka ɗaure su ko aka ci su tara ko aka yi masu wani hukuncin ko kuma aka dakatar da su a Amurka, Turai, da Asiya, a cikin ‘yan shekarun nan.
Ya ce, “Changpeng Zhao, hamshaƙin biloniyan nan kuma tsohon shugaban kamfanin Binance, wanda tare da shi aka kamfanin, a halin yanzu ya na zaman gidan waƙafi na tsawon watanni huɗu a Amurka, bayan da aka same shi da laifin almundahanar kuɗaɗe, yayin da Binance ya fito fili ya amince da rawar da ya taka wajen tallafa wa ayyukan ta’addanci, cin hanci da rashawa, daƙile takunkumi, da kuma taimaka wa da tallafa wa ƙungiyoyi masu lalata da ƙananan yara.
“Hukumomin doka da oda sun yi imanin cewa ayyukan Binance a Nijeriya wani ɓangare ne na rawar da kamfanin ke takawa a ƙasashen duniya. A nan ne kotuna, kamar yadda ake yi a sauran wurare, za su yi wa kamfanin da shugabannin sa hisabin da ya dace da su.”