Zamfara ta yi wa jihohin Arewa zarra a jarabawar NECO

Jihar Zamfara ta zama jihar da ta fi kowace jiha a Arewacin Nijeriya, kuma ta zamo ta biyu a faɗin Nijeriya a jarrabawar da Hukumar Jarrabawa ta Ƙasa (NECO), ta ke shirya wa ɗalibai ’yan baiwa a Nijeriya.

A makon da ya gabata ne Hukumar shirya jarabawar ta ƙasa ta fitar da Sakamakon Ɗalibai Masu Hazaƙa na 2024 don shiga Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Suleja.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar a ranar Lahadi, ya ce jihar Zamfara ce ta samu mafi yawan gurbi, inda ta zama jihar da ta yi fice a faɗin Arewa.

Ya ƙara da cewa, a faɗin ƙasar nan Zamfara ta zo ta biyu da haziƙan ɗalibai 30, yayin a jihar Anambra ta samu matsayi na ɗaya da ɗalibai 35.

“Ɗaliban Jihar Zamfara sun samu mafi girman maki a jarabawar NECO na ɗalibai masu hazaƙa a cikin jihohin Arewa 19, wanda hakan ya haifar da wani gagarumin ci gaba a ɓangaren ilimin jihar.

“A karon farko jihar Zamfara ta yi fice a matakin ƙasa, wanda ke nuna gagarumin sauyi daga matsayin da ta saba samu.

“NECO tana shirya jarabawar yara haziƙai da ‘yan baiwa domin samun gurbin karatu a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Suleja. ’Yan makarantar Firamare na shekarar ƙarshe ne kawai kuma ‘yan ƙasa da shekara 11 za su iya rubuta jarabawar, a Disambar shekarar jarabawar.”

Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Suleja, makaranta ce da ake horar da yara ’yan baiwa da masu hazaƙa a Nijeriya. Tana ƙara buɗe damarmaki ga ɗalibai ‘yan baiwa don haɓaka iyawarsu cikin sha’awar gina ƙasa da ci gaban fasaha.

Ɗaliban za su amfana da tallafin karatu na Gwamnatin Tarayya ta hanyar koyarwa, kuɗaɗen jarrabawa, wurin kwana, ciyarwa, kayan makaranta da litattafai.

“A shekarar 2024, Zamfara ta samu gurbi uku bisa ƙa’ida ta jiha kuma ta samu ƙarin gurbi 27 bisa la’akari da cancantar matsayinta a cikin tattalin arzikin Gwamnatin Tarayya. Ɗaliban Zamfara sun yi fice a jarrabawar, inda suka samu gurbi fiye da kowace jiha a Arewa.

“Wannan babban ci gaba ne, musamman idan aka yi la’akari da cewa an kafa dokar ta-ɓaci a fannin ilimi a jihar a bara.

“A cikin yara 30 masu hazaƙa daga Zamfara, 21 mata ne, 9 kuma maza ne, wanda hakan ke nuni da yadda ake ƙara ƙarfafa ilimin ‘ya’ya mata a jihar.

“Gwamnatin Jihar Zamfara za ta ci gaba da yin ƙoƙari wajen ganin an aiwatar da cikakken manufofin ilimi, wanda hakan zai sa a samu ƙarin nasarori ga jihar.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *