.
.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin ainihin misalin juriya, jarumta, da jajircewa waɗanda suka bayyana tarihin kafafen yaɗa labarai na Nijeriya tun farkon tafiyar dimokiraɗiyya a ƙasar nan.
Da yake jawabi a Taron Editocin Nijeriya na 2025 (ANEC) da aka gudanar a Abuja ranar Laraba, wanda ya kasance karo na farko da wani shugaban ƙasa mai ci ya halarta, Ministan ya ce halartar Shugaban Ƙasa Tinubu wata alama ce mai ƙarfi ta girmamawa da haɗin kai da ‘yan jaridar Nijeriya.
A cewar sa: “Rayuwa da jagorancin Shugaban Ƙasa na ɗauke da irin ƙarfin hali da jarumtar da suka bayyana aikin jarida a Nijeriya tun asali. Kamar dai kafafen yaɗa labarai, Shugaban Ƙasa ya kasance a kan gaba wajen kare gaskiya, dimokiraɗiyya da haƙƙin jama’a na a saurare su. Labarin sa da na kafafen yaɗa labarai a Nijeriya abu guda ne – tarihin juriya da tsayin daka.”
Idris ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu tana ci gaba da nuna amincewa da kafafen yaɗa labarai a matsayin abokan hulɗa wajen sake gina ƙasa. Ya jero wasu daga cikin sauye-sauyen tattalin arzikin da ake aiwatarwa kamar cire tallafin mai, daidaita farashin naira, da kuma shirin sabunta tsarin haraji, waɗanda a cewar sa suna daga cikin matakan da za su tabbatar da ɗorewar bunƙasar tattalin arziki.
Ya ƙara da cewa: “Ana ɗaukar matakai masu wahala amma da muhimmanci don gina ƙasa mai ƙarfi. Irin wannan ya yi nasara a Legas, kuma da rahoton ku na gaskiya da adalci, zai yi nasara a Nijeriya ma.”
Ministan ya sake jaddada aniyar gwamnati wajen kare ‘yancin kafafen yaɗa labarai, inda ya bayyana cewa fiye da tashoshin rediyo da talbijin 1,000 ke aiki a faɗin ƙasar nan ba tare da tsangwama ko takunkumi ba.
Ya ƙara da cewa tun bayan hawan mulkin Shugaba Tinubu, babu wata kafar yaɗa labarai da aka rufe ko aka hukunta saboda bayyana ra’ayin ta.
Ministan ya jaddada cewa amincewar duniya da Nijeriya a fannin yaɗa labarai tana ƙaruwa, inda ya kawo misalin kafa Cibiyar Ilimin Kafafen Yaɗa Labarai ta Duniya (IMLI) a Nijeriya, wanda ya ce zai ƙara bayyana ƙasar a matsayin jagora a nahiyar Afrika wajen yaɗa sahihan bayanai da aikin jarida na ƙwarai.
Ya roƙi ‘yan jarida, musamman editoci, da su ci gaba da zama abokan cigaban ƙasa, tare da bayyana gaskiya, adalci, da kyakkyawar fata a labaran su.
Ya ce, “Wannan gwamnati ta yi imani da ƙarfin kafafen yaɗa labarai wajen tsara tunani da ƙarfafa fata. Muna gayyatar ku da ku shiga cikin tattaunawa mai fa’ida, ku yi suka cikin girmamawa, kuma ku haɗa kai da gwamnati wajen zurfafa dimokiraɗiyya.”
Ya ce haɗin kai tsakanin gwamnati da kafafen labarai muhimmi ne wajen bunƙasa haɗin kan ƙasa da cika alƙawarin Shirin Sabunta Fata.
