Hukumar kula da harkokin man fetur (Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority – NMDPRA) ta bayyana cewa ba za a aiwatar da kudirin karin harajin kashi 15 cikin dari kan shigo da man fetur (PMS) da dizal ba.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, George Ene-Ita, ya fitar a shafinsu na X (da aka fi sani da Twitter) a ranar Alhamis, inda ya ce aiwatar da harajin da aka tsara baya cikin tsarin gwamnati a halin yanzu.
Hukumar ta tabbatar da cewa akwai wadataccen isasshen man fetur, dizal da iskar gas (LPG) a kasar, wanda ake samu daga masana’antun cikin gida da kuma shigo da su daga waje, domin biyan bukatar al’umma musamman a lokacin bukata ta musamman.
NMDPRA ta bukaci ‘yan kasuwa da masu motoci da su guji boye mai, saye da fargaba ko kuma kara farashi ba bisa ka’ida ba, tana mai cewa za ta ci gaba da sa ido a kasuwa tare da daukar matakan da suka dace domin tabbatar da cewa babu tangarda wajen rabon man.
“Hukumar na godewa dukkan masu ruwa da tsaki a sashen man fetur bisa kokarinsu na tabbatar da isar mai ba tare da katsewa ba, kuma muna tabbatar da aniyar mu na kare tsaron makamashi a kasa,” in ji sanarwar.
