Abubuwan da Isra’ila ta lalata a Gaza sun fi karfin na dalar Amurka biliyan 30

Ofishin kafar watsa labarai na gwamnatin Gaza ya ce abubuwan da suka lalace a dalilin Isra’ila a yankin da ya afka cikin yaki tun 7 ga watan Oktoba sun fi karfin na dalar Amurka biliyan 30 sakamakon dameji ga gidaje da sauran abubuwa da suka hada da wutar lantarki, ruwa da magudanan ban daki.

Kamar yadda The New Arab ta ruwaito, tun da Ifari dama ofishin ya ce watanni biyar da fara yakin, kashi 80 cikin 100 na gidajen Gaza an mayar da su “wadanda ba za a iya zama a ciki ba.”

A wani bangaren, kafar watsa labarun ta ruwaito cewa Isra’ila ta kai hari ga ginin da ke dauke da gidajen jama’a mafi girma a Rafah, Burj al-Masri, da ke kudancin zirin Gaza a ranar Asabar, kamar yadda mazaunan suka bayyana, inda ta ke kara matsi ga yankin da ya ke shine kawai ba ta kutsa ba kuma wanda ya ke dauke da Falasdinawa da suka bar muhallansu sama da miliyan daya wadanda ke samun mafaka.

Daya daga cikin mazauna ginin ya shaidawa Reuters cewa Isra’ila ta ba su mintuna 30 ne kawai na gargadi su bar ginin.

“Mutane sun girgiza, suna saukowa da gudu daga kan matakalar bene, wasu sun fadi, rudani ne kawai. Mutane sun bar kayayyakinsu da kudadensu.” Kamar yadda Mohammad Al-Nabrees ya bayyana, inda ya kara da cewa cikin wadanda suka fadi a kasan matakalar bene a yayin gujewa ginin cikin firgici akwai matar abokinsa wadda ke da ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *