Ambaliyar Jebba Dam ta lalata gonaki hekta 1,094 da ke jihar Neja – Hukumar NEMA

Daga Abubakar Musa

Ambaliyar ruwa daga Jebba Dam ta lalata gonaki 1,094 a al’ummu 32, inda hakan ya shafi manona 544 a karamar hukumar Mokwa da ke jihar Neja.

Kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito, ambaliyar wadda ta faru ta shanye tare da lalata gonakin noman rani na shinkafa da ke bakin Rafin Neja wanda hakan ya haifar da asara mai yawa.

Hukumar agajin gaggawa (NEMA) ofishin jihar Neja a cikin wani jawabi ta bayyana cewa ta kaddamar da tattara bayanai kan al’ummu da gonakin da al’amarin ya shafa a ranar 6 ga watan Fabrairu.

NEMA ta tabbatar da cewa ambaliyar ta yi mummunar shafar manoma, inda ta lalata hatsi tare da mayar da fili Mai girman gaske ba za a iya amfani da shi ba.

Wasu manoman da al’amarin ya shafa sun shaidawa Sahara Reporters cewa Jebba Dam ya kan saki ruwa ne mafiyawanci a lokacin damina, kuma a kan yi masu nuni da hakan wata biyu kafin hakan ya faru – mafiyawanci a watan Augusta da Satumba. Amma, a wannan karon, babu gargadin da aka yi kafin dam din ya saki ruwan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *