Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa kiran da Ƙungiyar Gwamnonin PDP ta yi wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ya yi murabus ba komai ba ne illa wani yunƙuri na karkatar da hankalin jama’a daga mutanen da ya kamata su shagaltu da tallafa wa ƙoƙarin shugaban ƙasa na kawo wa al’ummar Nijeriya agajin gyaran tattalin arziki.
A cewar sa, bai kamata PDP da gwamnonin ta su riƙa nema, ta hanyar tsoratarwa, abin da su ka kasa cimmawa ta hanyar dimokiraɗiyya tun cikin 2015.
A wata sanarwa da mai ba shi shawara kan aikin jarida, Rabi’u Ibrahim, ya bayar, Idris ya ce: “Bai kamata waɗanda su ka gaza kawo sauyi a lokacin da su ka samu dama mai tsawo ba su nemi katsewa ko karkatar da hankalin masu aiki kan manufar shugaban ƙasa da ‘yan Nijeriya su ka zaɓe su don aiwatarwa ba.
“Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, tun da aka kafa ta, ta ba da tallafin kuɗi ga dukkan gwamnatocin jihohi, ba tare da la’akari da ɓangaranci ba.
“Kazalika, cire tallafin man fetur, wanda aka yi ba zato ba tsammani, ya na ɗaya daga cikin manyan ginshiƙan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, wato don ya ƙara kuɗaɗen shiga na ɗaukacin jihohi, ciki har da jihohin PDP. Wanda aka ba da yawa, ana sa ran samun da yawa daga wurin shi.”
Ministan ya ce, “Shugaban Ƙasa da gwamnatin sa sun amince da ayyukan da ba a kammala ba na farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar mu da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta fara, ta hanyar shirye-shiryen da su ka mayar da hankali kan manyan ababen more rayuwa, walwala da jin daɗin jama’a, da ba da fifiko wajen samar da kayan aiki da kyautata wa sojoji da hukumomin tsaro, da kuma maido da Nijeriya turbar matsayi mai mahimmanci a tsakanin ƙasashe.”
Ya yi nuni da cewa tun daga shekarar 2014/2015 aka kawo ƙarshen Boko Haram da masu alaƙa da su, kuma a halin yanzu ana samun irin wannan gagarumar nasarar a kan ‘yan bindiga da sauran miyagun mutane.
A cewar sa, ‘yan Nijeriya dai ba su manta da cewa gwamnatin APC ce ta kawar da naƙasu da dama da gwamnatin PDP ta bari a baya ba, kamar neman tallafin man fetur da ‘yan kasuwar man fetur ke yi, da dawo da kuɗaɗen Paris Club, biyan fansho da ba a biya ba, da kuɗaɗen sallama daga aiki, da basussukan albashi da ake bin kashi daban-daban na ’yan fansho daga kamfanoni mallakar gwamnati da aka sayar da kuma waɗanda ake da su a yanzu.
Ya ce: “Manyan sauye-sauye a ɓangaren man fetur da PDP ta dinga tallatawa na tsawon shekaru amma ta kasa cimmawa – ƙaddamar da Dokar Masana’antar Man Fetur (PIB), sababbin matatun mai, da kuma sake fasalin waɗanda ake da su, da sauran su – su ne ainihin abubuwan da jam’iyya mai mulki ta APC ta yi.
“Dukkan waɗannan an yi su ne ba tare da samun ribar man fetur da gwamnatin PDP ta ci a tsawon lokacin da ta ke kan karagar mulki ba, sannan kuma a lokacin annobar COVID-19.
“Dole ne mu ci gaba da bayyana waɗannan hujjoji domin ’yan Nijeriya su san daga inda mu ke, kuma su yaba da abin da ake yi.
“Shugaba Tinubu ba zai taɓa gajiyawa da ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta a halin yanzu ba. Ba zai yi watsi da nauyin da ke kan sa ba, da jajircewa zai ci gaba da kokawa da shawo kan ƙalubalen da ke gaban sa, tare da aza harsashi mai ɗorewa ga sabuwar Nijeriya da ke tasowa.
“Har ila yau, ba zai ce bai san raɗaɗin sauye-sauyen da ake ci gaba da yi ba, ya kuma yi amfani da duk wata dama da za ta samu wajen tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa raɗaɗin sauye-sauyen ya ta’allaƙa ne da samar da arziki mai ɗorewa da cigaban ƙasa.
“Ga gwamnonin PDP, bari mu sake nanata cewa: Wannan ba lokacin da za a raba hankali ba ne. Lokaci ya yi da za a yi shirin aiki, don tallafawa da cika aikin Shugaban Ƙasa da gwamnatin sa.”