An fara tattaunawa dangane da tsagaita wuta kashi na biyu – Hamas

Mai magana da yawun kungiyar Hamas, Abdul Latif al-Kanou, ya bayyana cewa an fara tattaunawa kan yarjejeniyar tsagaita wuta kashi na biyu.

Kamar yadda ya ke a wani rahoto na kafar watsa labaru ta The New Arab, yarjejeniyar tsagaita wuta ta farko a tsakanin Hamas da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta fara aiki ne a ranar 19 ga watan Janairu bayan kwashe watanni 15 na yaki, ta kuma kunshi tsayar da yakin, sako wasu ‘yan Isra’ila da Hamas ke ruke da su da kuma sako wasu Falasdinawa.

Kashi na biyu na yarjejeniyar wadda ke da kashi har uku na da niyyar mayar da hankali ne wajen sakin sauran wadanda aka yi garkuwa da su da kuma janyewar sauran sojojin HKI daga Gaza.

Ofishin Firaministan HKI Benjamin Netanyahu ya bayyana a farkon ranar Talata cewa HKI na shirin tura manyan jami’ai zuwa babban birnin kasar Katar, Doha, domin cigaba da tabbatar da faruwar yarjejeniyar.

Netanyahu na da shirin tattaunawa da shugaban kasar Amurka Donald Trump a ranar Talata, inda tattaunawar akwai yiwuwar ta mayar da hankali a kan tsagaita wuta da kuma yiwuwar daidaita dangantaka da kasar Saudi Arabiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *