An sa ranar yanke hukunci ga dan China da ake zargin ya kashe budurwarsa a Kano

Wata babbar kotu a jihar Kano ta sa ranar shari’ar da ta hada da Geng Quangrong , wani dan kasar Sin da ake zargin ya kashe budurwarsa ‘yar Nijeriya, Ummukulsum Sani, mai shekaru 22.

Kamar yadda PM News ta ruwaito, Quangrong, wanda ke zaune a Railway Quarters Kano, ana zarginsa ne da aiwatar da abinda ya kai ga kisa. Sai dai, ya musanta zargin da ake yi masa.

Alkali Sanusi Ado-Ma’aji, ya dage al’amarin shari’ar har sai ranar 29 ga watan Maci.

Dage shari’ar na zuwa ne bayan tabbatar da rubutun wadanda suke a matsayin masu hukunci da kuma kariya, Muhammad Dan’azumi da Aisha Mahmoud.

Mai hukuncin ya kulle shari’ar a kan wanda ake zargin bayan ya kawo shaidu shida a ranar 21 ga watan Disambar shekarar 2022.

Shima wanda ake karar ya kulle shari’arsa da shaidu biyu, cika har da “urologist” Dakta Abdullahi Abubakar.”

A cikin jawabinsa, Quangrong, ya shaidawa kotu cewa Ummukulsum ta kai masa hari da wuka.

“Yayin da na ke kare kai na, Ummukulsum ta cijeni a kafada ta sannan ma ta ji min ciwo a gabana.” Kamar yadda Quangrong ya bayyana.

Wanda ake karar an yi ikirarin cewa ya yanki wadda ta rasu din ne da wuka a gidan ta da ke Janbulo Quarters Kano a ranar 16 ga watan Satumbar shekarar 2022. Laifin, kamar yadda mai yanke hukuncin ya bayyana, ya sabawa tanadin sashe na 221(b) na dokar Panel Code.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *