Daga Nasir Isa Ali
Dakarun Hizbullah da ke kudancin Lebanon sun sami nasarar kashe wani tsohon Bayahude da ya dade yana yin ta’adda ga al’ummar musulmin yankin, sailin da ya shiga cikin wasu rundunar sojan mamaya a tsakiyar makon nan.
Ashe shi wannan tsohon bayahude Dan Shekara 71 a duniya Mai suna Zeer Ehrlich Jabo ya kwashe kimanin shekaru 40 Yana zana wa kasar Binyaminu inda za su rika mamayewa.
Duk inda sojojin Netanyahu za su je yin aika aika, to da shi a cikin su domin wai ya kara shata musu inda za su mamaye da kuma wadanda za a kashe ko a kore su daga garuruwansu saboda su kara fadada kasar tasu ta mamaya.
Tun da aka fara wannan yakin Guguwar, babu inda ba ya bin sojojin mamaya domin ya kara gano musu inda za su mamaye.
Shi ne ya rubutawa Netanyahu gariruwan da za’a mamaye a kudancin Lubnan.
Sai jiya dubunsa ya cika, inda ya bi kwararrun sojojin Netanyahu zuwa Kudancin Lubnan, inda shigarsu wani kauye ke da wuya aka aika shi da abokansa ‘yan mamaya zuwa lahira.