An Yi Bikin Kaddamar Da Makarantar Khatamul Anbiya Institute of Islamic Science A Kano

An yi bikin kaddamar da Cibiyar kimiyyar Musulunci wacce aka fi sani da Khatamul Anbiya Institute of Islamic Science dake garin Kano. Bikin kaddamarwar ya gudana ne a ranar Asabar 9 ga watan Maris 2024, a harabar makarantar dake karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano.

Taron ya soma gudana ne da bude taro da addu’a wanda Sayyid Khidir ya gabatar. Sai karatun Alkur’ani mai girma wanda daya daga cikin daliban ya karanta.

Injiniya Muhammad S. Shu’aibu, Rijistira na makarantar, ya gabatar da jawabin makasudin kafa wannan makaranta. Inda a cikin jawabinsa ya ce; “A yau ba wai kawai mun taru ne domin bikin kaddamar da cibiyar ilimi ba, wannan wata guguwar sauyi ne – wanda ke ƙoƙarin sake fasalin yadda ake fahimtar addini, ilimi, da kuma tasirin su ga al’ummar mu da ƙasa gaba ɗaya.

A yayin da yake bayyana makasudin wannan makaranta, Injiniya Shuaibu ya ce; “Sabanin yadda ake fahimtar addini a kaikaice, addinin gaskiya wanda Annabin Musulunci Manzon Allah (S) ya koyar, ya koyar da tausayi, jin kai da kuma mutunta juna. A cikin wannan yanayin ne aka samar da makaranta ta Khatamul Anbiya – wanda wani kyakkyawan shiri ne da wasu ’yan Nijeriya masu kishin kasa da himma dake son bayar da kyakkyawan gudunmawa wajen gina kasa ta hanyar samun zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai daban-daban. Wannan aiki ya ta’allaka ne da zurfin tunani na isar da koyarwar Musulunci a dukkan zurfinsa da fadinsa, tare da jaddada tsarin hakuri, tattaunawa a tsakanin al’ummomi, da mutunta ra’ayoyi daban-daban.

Ya ci gaba da cewa; “A yayin gudanar da wannan gagarumin aiki na Khatamul Anbiya muna masu mika hannun sada zumunci da ‘yan uwantaka ga duk wani dan Nijeriya mai kishin kasa. A don haka muna gayyatar ku da ku kasance da mu a cikin wannan manufa mai albarka – tafiya ce dake dinke barakar dake tsakanin al’ummar Musulumi domin hadin kai, mutunta juna, kuma makami ne mai karfi na gina kasa”.

Rijistiran ya ce; manufarsu ba za ta tsaya a nan kadai ba, suna yunkurin samar da Jami’ar Khatamul Anbiya da za ta yi gogayya da sauran jami’o’i.

“Yana da muhimmanci a gane cewa wannan cibiyar ba ita ce ƙarshe ba, ba kuma a nan ta tsaya ba, tana da faɗi kuma muna aiki tukuru wajen fadada ta. Tunaninmu ya wuce iyakar wannan cibiya, muna da burin haɓakawa zuwa cikakkiyar jami’a mai daraja da ƙima. Wannan jami’a mai zuwa da za a fi sani da Jami’ar Khatamul Anbiya, za ta kasance fitilar fahimtar juna ta addini, ta yadda za ta samar da daidaikun mutane masu ilimi da tarbiyyah a ma’anar Musulunci”, ya jaddada.

A ƙarshe, ya kuma jaddada manufar samar da wannan cibiya ta ilimi, inda ya ce; “Cibiyar Khatamul Anbiya ta kasance a matsayin shaida na hadin kanmu na ganin mun samar da muhallin da ilimi ya keta shingaye, da dinke banbamce-bambancen dake tsakanin al’umma, kuma hakikanin koyarwar Musulunci shi ya shiryar da mu baki daya zuwa ga mu kasance al’umma mai fahimtar juna.

Bayan ya kammala jawabinsa, shugaban makarantar, Dr Shuaibu Muhammad, ya gabatar da na shi jawabin cikin harshen Larabci, inda ya jaddada wadannan manufofi na makarantar.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin tallafawa wannan makaranta. Inda ya ce a baya ma gwamnatin jihar Kano ta tallafawa ire-iren wadannan makarantu. Gwamnan ya bayyana hakan ne ta hannun Kwamishinan ilimi na jihar, Umar Haruna Doguwa wanda ya wakilci gwamnan. “ina mai tabbatar wa da wannan makaranta cewa mai girma gwamna zai fadada wannan tallafi zuwa wannan makaranta. Muna yin wannan ne domin taimakon kowa da kowa”.

Bayan kammala jawabinsa, makarantar ta gabatar da kyauta ta musamman ga Mai Martaba Sarkin Sako, Alhaji Aminu Ado Bayero.

A cikin jawabin Mai Martaba, ya mika godiyarsa ga kafatanin mahalarta taron. Sannan ya nuna farin cikinsa bisa samar da wannan makaranta wacce za ta ci gaba da aikin koyar da ilimi da tarbiyyah. “Wannan makaranta wacce za ta ci gaba da aikin tarbiyyantar da ‘ya’yanmu da koyar da su addinin Musulunci. Ta yadda za su amfani kansu, su amfani ‘yan’uwansu”.

Mai Martaba ya ci gaba da cewa “muna matukar farin ciki da wannan manufa ta wannan makaranta. Kuma muna kira ga hukumomi da jama’a masu iko su hada hannu da wannan makaranta wato Khatamul Anbiya Institute of Islamic Sciences domin samun cin nasarar wannan kyakkyawan manufa.

“muna kuma kira ga al’umma da su yi kokarin kawo ‘ya’yansu domin su ci amfanin wannan alheri da ya zo musu suna zaune a gidajensu. Muna rokon Allah ya tallafi wannan manufa ta alheri ya bada ikon ci gaba da ita daga nan har zuwa inda Allah ya nufa.

Ya yi godiya bisa ga wadanda suka bada gudummawa da wadanda za su ci gaba da bada gudummawa a nan gaba na kafa Jami’a. Ya kuma kara da cewa; “A kullum muna maraba da dukkanin wadansu ayyukan alheri da za a bijiro da su da zai amfani al’ummar mu na Kano da ma kasa baki daya. Muna kira gare su su tabbatar wannan makaranta ta zama ta al’ummar wannan jiha baki daya. Dukkanin abin da za su gudanar ya zama bisa tafarki nagari ne da taimakon al’umma da taimakon addinin Musulunci”. A karshe ya sanya wa makarantar albarka.

Hakimin Nasarawa, ya gabatar da jawabin godiya. Daga karshe shugaban makarantar Dr Shuaibu ya gabatar da addu’ar rufewa. Daga nan Sarkin ya jagoranci bude makarantar.

Taron kaddamarwar ya samu halartar mutane da dama da ya hada da; Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, Kwamishinan Ilimi na jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, Daraktan Hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS ta jihar Kano, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Hakimai da Dagatai, da Malaman jami’o’i da sauran su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *