An yi satar fitar hankali a gwamnatin Elrufa’i


Majalisar dokokin jihar Kaduna ta buƙaci a bincike shi

Kwamitin da Majalisar dokokin jihar Kaduna ta kafa kan nazari game da kuɗaɗen da aka kashe a gwamnatin da ta gabata a jihar ya miƙa sakamakon bincikensa a yau.

Cikin shawarwarin da kwamitin ya bayar har da na buƙatar hukumomi su binciki tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufa’i.

Lokacin da ya gabatar da rahoton a ranar Laraba, shugaban kwamitin, Henry Zacharia ya ce an gano cewa akasarin kuɗin bashin da jihar ta karɓa a zamanin mulkin El-Rufa’i, ko dai ba a yi amfani da su kan abin da aka ciyo bashin domin su ba ko kuma ba a bi ƙa’ida wajen cin bashin ba.

Lokacin da ya karɓi rahoton, shugaban majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Liman ya ce kuɗi naira biliyan 423 ne suka zurare a lokacin gwamnatin El-Rufa’i tare da jefa jihar cikin ƙangin bashi.

Kwamitin ya buƙaci da a binciki tsohon gwamnan da wasu jami’an gwamnatinsa kan zargin rashawa da bayar da kwangila ba bisa ƙa’ida ba da kuma halasta kuɗin haram.
A watan Afrilu wannan shekara ne Majalisar dokokin jihar Kaduna ta kafa kwamiti domin binciken ayyukan da gwamnatin El-Rufa’i ta aiwatar tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023.

Hakan ya zo ne bayan gwamnan jihar, Uba Sani ya koka kan cewa jihar na fama da ƙangin bashin da ya kai na naira biliyan 85 da kuma wasu ayyukan da ke buƙatar kuɗi naira biliyan 115 domin kammalawa.

Uba Sani ya bayyana cewa a halin da ake ciki “jihar ba ta iya biyan albashi ba tare da ta ciyo bashi ba”.

Lamarin ya haifar da muhawara, ganin cewar a baya ana yi wa gwamna Uba Sani da tsohon gwamna Nasiru El-Rufai kallon aminan juna.

A shekarar 2023 ne Nasir El-Rufa’i ya miƙa ragamar mulkin jihar ta Kaduna ga Sanata Uba Sani, bayan kammala wa’adin mulkinsa na shekara takwas.

Uba Sani ya zama gwamna ne bayan ya lashe zaɓen da aka gudanar a watan Maris na shekara ta 2023.

Kafin wannan lokacin, Uba Sani ya kasance ɗan majalisar dattijai mai wakiltar mazaɓar Kaduna ta tsakiya, kuma ana ganin ya taka muhimmiyar rawa wajen karɓar basussukan da gwamnatin jihar Kaduna ta samu a lokacin mulkin Nasir El-Rufa’i.

Kaduna na daga cikin jihohin Najeriya waɗanda suka fi yawan bashi a kansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *