‘Yan Nijeriya sun kammala makon nan ta hanyar fitowa ba kaɗan ba a kan tituna a ranar Asabar domin gudanar da zanga-zangar lumana a Legas sakamakon hauhawar farashin kayan masarufi da ke damun ƙasar.
Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, masu zanga-zangar waɗanda aka bayyana cewa mata ne ‘yan kasuwa, maza da kuma matasa sun ɗauko kwalaye daban-daban zuwa yankin Ibeju-Lekki na jihar domin nuna ~acin ransu da gwamnati kan wahalhalun.
A yayin zanga-zangar a yankin Ibeju-Lekki da ke Legas, matan sun ɗauko kwalaye da aka yi rubutu kamar “Baba Tinubu, ‘yan Nijeriya na jin yunwa” da kuma “Tinubu, ka zo ka cece mu” da sauransu.
A cikin ‘yan kwanakin baya, wasu ‘yan Nijeriya sun hau kan tituna domin zanga-zanga a jihohin Kogi, Osun, Neja da Kano kan hauhawar talauci a ƙasa.
Tun bayan cire tallafin mai a watan Mayu na shekarar 2023, farashin kayayyaki ke ta yin sama a ƙasar.
Wani babban masanin shari’a a Nijeriya, Farfesa Itse Sagay, ya ce yadda shugaban ƙasa Bola Tinubu ya cire tallafin mai ba tare da ~ata lokaci ba a cikin jawabin rantsuwarsa a ranar 29 ga watan Mayun 2023, ya haifar da babbar wahala ga ‘yan Nijeriya.
Sagay, wanda ya yi aiki a matsayin shugaban kwamitin shugaban ƙasa na bayar da shawara a kan cin hanci a ƙarƙashin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana haka ne a wata tattaunawa wadda gidan talabijin ɗin Channels ya nuna a ranar Juma’a.