A karshen makon jiya ne Ayatullah Sayyid Ali Sistani, babban Marji’i da ke Najaf, Iraq ya fitar da sanarwa, inda yake Allah wadai da kisan da wasu jama’a suke yi wa ‘yan Shi’a a Pakistan.
Ya kuma nemi gwamnatin ƙasar da ta dakatar da bazuwar lamarin, tare da taimakon raunanan da abin ya shafa.
Ga fassarar sanarwar:
Sanarwa daga Ofishin Mai Daraja Ayatullah Sistani
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai.
“Lalle ne mu daga Allah ne, kuma zuwa gare Shi masu komawa ne.”
Zuwa ga ‘yan uwa muminai maza da mata mazauna birnin Parachinar Pakistan, Assalamu alaikum. Rahma, da albarkar Allah su tabbata a gare ku.
Ba’ada bayan haka, ‘yan ta’adda marasa zuciyar tausayi, sun aikata wani mummunan laifi, inda suka kai hari da makami kan matafiya da ke tafiya daga Parachinar zuwa Peshawar. Wannan harin ya yi sanadin shahada da raunata dimbin muminai da ba su ji ba, ba su gani ba.
Muna mika ta’aziyyarmu da ta’aziyya gare ku, ‘yan uwa, tare da shiga cikin alhinin iyalan wadanda suka rasu. Muna addu’ar Allah ya ba da hakuri da juriya ga kowa da kowa, da gaggawar samun lafiya ga wadanda suka jikkata, ya kuma daukaka darajojin shahidan wannan mummunan lamari.
Makarantar Hauza ta Najaf Ashraf da kuma hukumar kula da harkokin Shi’a na addini, a yayin da suke yin Allah wadai da wannan danyen aikin da ke da nufin kawo cikas ga hadin kan musulmi, sun bukaci gwamnatin Pakistan mai girma da ta dauki matakan da suka dace don tallafa wa al’ummar da ake zalunta wajen tunkarar zalunci da laifukan kungiyoyin ‘yan ta’adda. Ya zama wajibi a hana kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi, marasa tausayi daga kai wa wadanda ba su ji ba, ba su gani ba hare-hare na tashin hankali kuma na dabbanci.
Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya ci gaba da daukaka martabar al’ummar Pakistan.