Wasu Muhimman Kalaman Ministan Tsaro Mohammed Badaru Abubakar…
-A cikin shekaru biyu na gwamnatin Tinubu wadda ta tarar da ƙalubale mafi muni a tarihin ƙasashen Sahel, an sami cikakken tsaro a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna wanda a baya ya taɓa kasancewa tungar masu garkuwa da mutane.
-Daga watan Mayun 2023 zuwa yanzu mun yi nasarar murƙushe ƴan ta’adda har 13,000, kazalika an kawar da shugabannin Boko Haram sama da 300
-A Maiduguri, a baya da an ce Gambaru, Bama, ka san an ambaci hanya mai hatsarin gaske, amma a yanzu hakan ya zama tarihi, duk wannan ya faru ne a cikin shekaru 2 na wannan gwamnatin