Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) da ta amince da mafi ƙanƙantar albashi na ƙasa wanda ba zai gurgunta tattalin arzikin ƙasa ba, kuma ya kai ga korar ma’aikata da dama.
Idris ya yi wannan roƙo ne a lokacin da yake buɗe taron ƙungiyar limaman Kirista ta Charismatic Bishops of Nijeriya na 2024 a Abuja ranar Laraba.
A cikin wata sanarwa da Mataimaki na Musamman ga Ministan kan Harkokin Yaɗa Labarai, Rabi’u Ibrahim ya fitar, an ruwaito cewa Idris ya jaddada buƙatar samar da ingantaccen tsarin albashi mai ɗorewa wanda zai daidaita buƙatun ma’aikata da yanayin tattalin arzikin ƙasa.
Ya bayyana ƙudirin gwamnati na sake duba mafi ƙanƙantar albashi amma ya yi gargaɗi kan buƙatu da ka iya cutar da tattalin arzikin ƙasar nan.
Ministan ya bayyana ƙoƙarin da gwamnati ke yi na rage tsadar rayuwa da kuma ƙara wa ‘yan Nijeriya ƙarfin yin sayayya ta hanyar shirye-shirye kamar shirin Shugaban Ƙasa na samar da motoci masu aiki da gas (CNG), wanda ke da nufin rage kuɗin sufuri da kashi 50 cikin ɗari.
Ya ce: “Kamar yadda na sha faɗa, Gwamnatin Tarayya ba ta adawa da ƙarin albashi ga ma’aikatan Nijeriya amma muna ci gaba da bayar da shawarwarin samar da ingantaccen tsarin albashi ga ma’aikata – tsarin albashin da ba zai gurgunta tattalin arzikin ƙasa ba har ya kai ga korar ma’aikata da yawa tare da kawo cikas ga jin daɗin ‘yan Nijeriya kusan miliyan 200.
“Muna so ‘yan Ƙungiyar Ƙwadago su fahimci cewa sauƙin da ‘yan Nijeriya ke jira, kuma suka cancanta a ba su, ba zai zo ne kawai ta hanyar ƙarin albashi ba.
“Zai zo ne kuma a ƙoƙarin rage tsadar rayuwa da kuma tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya sun samu ƙarin kuɗaɗe. Kuma a nan ne shirye-shirye kamar shirin CNG na Shugaban Ƙasa ke shigowa.
“Ta hanyar maye gurbin amfani da man fetur da iskar gas, wannan shirin kaɗai zai rage kuɗin sufuri da kashi 50 cikin ɗari.”
Ministan ya yi kira ga malaman addinin Kirista da su goyi bayan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu wajen ganin an farfaɗo da Nijeriya tare da yin addu’ar hikima da jagora a daidai lokacin da ƙasar nan ke fuskantar ƙalubalen da ke addabar ta.
“Haƙiƙa, Coci, a tsawon tarihin ƙasar mu, ta kasance abokiyar hulɗa ga gwamnati wajen fafutikar tabbatar da zamantakewa da samar da muhimman ayyukan jin daɗin jama’a kamar asibitoci da makarantu, da kuma cusa ɗabi’u na gari a cikin ‘yan ƙasar mu.
“Ko da muna cikin mawuyacin hali na wucin-gadi amma wanda ya zama dole, ba hutu Shugaban Ƙasa ke yi ba. Ya ƙudiri aniyar tabbatar da cewa an fitar da matakan agaji da dama domin amfanin kowane ɓangare na al’ummar Nijeriya.
“Yanzu, a nan ne ku a matsayin ku na malaman addinin Kirista, a matsayin ku na shugabannin addini da ake mutuntawa da kuma masu faɗa a ji, za ku shigo. A matsayin mu na gwamnati, muna buƙatar goyon bayan ku, shawarwarin ku, da ra’ayoyin ku.
“Abu mafi muhimmanci kuma shi ne muna buƙatar ku san ƙoƙarin da ake yi, da ƙalubalen da ake fuskanta, domin ku taimaka mana mu sanar da waɗannan ikilisiyoyin ku da sauran jama’a.”
Yayin da ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya hau karagar mulki ne a lokacin da aka fi fuskantar ƙalubale a Nijeriya, Idris ya ce Shugaban Ƙasar na bakin ƙoƙarin sa wajen ganin an samu cigaba mai ɗorewa a faɗin ƙasar nan.
Ya ce: “Babu wanda ke shakkar cewa Shugaban Ƙasa ya tashi tsaye ne tare da jajircewa da aikata abin da ya dace. A cikin shekarar da ta gabata ya aiwatar da muhimman gyare-gyare masu muhimmanci da nufin mayar da ƙasar mu kan turbar haɓaka, wadata, da samun cigaba mai ɗorewa.
“Shugaba Tinubu bai taɓa ƙin amincewa da gaskiyar wannan raɗaɗin da ake ji ba. A cikin jawabin sa na Ranar Dimokiraɗiyya da ya gabatar wa al’ummar ƙasar da safiyar yau, Shugaba Tinubu ya taƙaita shi da kyau da ya ce: ‘Mun ɓullo da gyare-gyare ne domin samar da tushe mai inganci don samun cigaba a nan gaba.
“Babu shakka sauye-sauyen sun haifar da wahalhalu. Amma duk da haka, su ne gyare-gyaren da ake buƙata domin gyara tattalin arziki cikin dogon lokaci ta yadda kowa zai samu damar tattalin arzikin, da samun albashi mai kyau, da kuma ladar ƙoƙarin sa da ayyukan sa.'”
Idris ya ƙara da cewa: “Haƙiƙa, a matsayin mu na al’umma, muna jure wa sadaukarwa na ƙanƙanen lokaci domin samun fa’ida ta dogon lokaci. Mun samu ƙwarin gwiwa da Nijeriyar da ba za a bar kowa a baya ba.”
Ya yi nuni da cewa ma’aikatar sa za ta haɗa kai da malaman Kirista wajen aiwatar da shirin wayar da kan jama’a na ƙasa, wato ‘National Values Charter’.
“Saboda haka, bari in ce Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai za ta yi matuƙar farin ciki da haɗa kai da babban Taron Charismatic Bishops yayin da muke aiwatar da shirin mu na wayar da kan jama’a, wato ‘National Values Charter’, wanda ke neman cusa ɗabi’u masu ɗorewa a cikin zukata da tunanin ‘yan ƙasar mu”, inji shi.
Ya jaddada cewa Shugaba Tinubu ya aiwatar da manufofin sa na Sabunta Fata yayin da ‘yan Nijeriya ke ci gaba da samun ƙarin nasarori a sassa daban-daban na tattalin arzikin mu.
“Shugaban Ƙasa ya yi aiki tuƙuru don daidaita tattalin arzikin ƙasar ta hanyar janye tallafin man fetur maras ɗorewa da kuma haɗewar kasuwar canjin kuɗaɗe, a matsayin muhimman matakai na karkatar da kuɗaɗe zuwa sassa masu mahimmanci kamar kiwon lafiya, ilimi, da ababen more rayuwa.”
Tun da farko, sai da Shugaban ƙungiyar ‘Charismatic Bishops Conference’ na Ƙasa, Archbishop Leonard Bature Kawas, ya yi alƙawarin biyayya da goyon baya ga gwamnatin Shugaba Tinubu, tare da jaddada cewa za su ci gaba da haɗa kai da gwamnati domin cimma burin ta ga Nijeriya.
Ya ƙara da cewa sun gayyaci ministan wanda Musulmi ne domin ya buɗe taron nasu saboda suna ga cewa ɗan Nijeriya ne mara ƙabilanci wanda ba ya nuna bambancin addini.
Archbishop Kawas ya ce limaman coci daga jihohi 36 na tarayya da ƙasashe 21 ne suka halarci taron.