
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya ɗaukacin al’ummar Musulmi murnar zagayowar ranar Babbar Sallah, ya ce lamarin wanda ke nuni da sadaukarwa, ɗabbaka imani da biyayya ga nufin Ubangiji.
A wata sanarwa da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Ajuri Ngelale ya fitar, Shugaban Ƙasa ya taya al’ummar Musulmi murna tare da addu’ar Allah ya karɓa masu addu’o’in su da kuma ayyukan su na alheri.
Haka kuma ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi tunani a kan maudu’in bikin, wanda ke da ma’ana mai ƙarfi da muhimmancin ga ƙasar nan.
Ya jaddada cewa sadaukarwa da aiki su ne muhimman sinadiran gina ƙasa, ya na mai cewa sai an yi nufi da aiki tare domin kawo sauyi mai girma.
Shugaban ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi wa ƙasar nan addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da yin aiki wajen inganta haɗin kai, zaman lafiya da cigaba.
Ya yi la’akari da sadaukarwar da ’yan Nijeriya su ka yi a cikin shekara ɗaya da ta gabata yayin da gwamnatin sa ta sanya ƙasar a kan turbar haɓaka da cigaba.
Ya kuma tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa gwamnatin sa na ba da fifiko ga tsaron lafiyar su ta jiki, ta zamantakewa da kuma tattalin arziki, ya ce ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba kan wannan kyakkyawan aiki.
Shugaban ya yi wa ‘yan Nijeriya fatan murnar bikin Sallah.