Cire Tallafin Man Fetur: Minista Ya Yaba Wa IPMAN Don Rungumar Shirin CNG

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yaba wa Ƙungiyar ‘Yan Kasuwar Man Fetur Masu Zaman Kansu (IPMAN) bisa namijin ƙoƙarin da suke yi na ganin an fito da tsarin samar da makamashi na wanda Ba man fetur ba da Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da shi bayan cire tallafin man fetur da Shugaba Bola Tinubu ya yi.

Idris, wanda ya bayyana hakan a lokacin da ya karɓi baƙuncin kwamitin gudanarwa na IPMAN na ƙasa a ofishinsa da ke Abuja a ranar Alhamis don ziyarar ban-girma, ya ce Gwamnatin Tarayya na da burin rage farashin sufuri da sama da kashi 50 cikin ɗari ta hanyar shirin amfani da motoci masu aiki da iskar gas (CNG Initiative).

“Bayan cire tallafin man fetur, ba shakka ana tsammanin farashin man fetur zai hauhawa. Hakan kuma zai shafi farashin sufurin da ‘yan Nijeriya ke kaiwa da komowa a wuraren ayyukansu daban-daban.

“Nan da nan Gwamnatin Tarayya ta yi tunanin cewa ya kamata, ban da wasu matakan, ta ɓullo da CNG. Ana sa ran CNG zai rage farashin sufuri da sama da kashi 50 cikin ɗari, kuma ina farin cikin cewa IPMAN na kan gaba wajen ganin an cimma nasarar shirin CNG ɗin,” inji shi.

Ministan ya ce matakin da Shugaba Tinubu ya ɗauka na cire tallafin man fetur ya ba da dama ta musamman ga ƙungiyoyi irin su IPMAN da za su kasance kan gaba wajen tsara yanayin makamashi a Nijeriya.

Ministan ya ce Nijeriya a matsayinta na ƙasa ta na neman wasu hanyoyin da za ta rage farashin sufuri kuma CNG ita ce hanya mafi inganci da za a bi.

Idris ya ce tuni Gwamnatin Tarayya a matakin farko ta ware naira biliyan 100 domin sayen motocin bas ɗin CNG da kuma kafa cibiyoyin CNG a faɗin ƙasar nan.

Ya ce wannan yana baya ga ɓullo da dokar hana biyan haraji ga masu shigo da kaya na CNG da sauran masu saka hannun jari a wannan ɓangaren.

“Za ku iya tunawa Gwamnatin Tarayya tun farko ta ware naira biliyan 100 don sayen motocin bas na CNG da kuma kafa cibiyoyin CNG a faɗin kasar nan,” inji shi.

Yayin da yake neman goyon bayan ƙungiyar IPMAN ɗin domin samun nasarar shirin Sabuwar Fata na Shugaba Tinubu, ministan ya yi masu godiya bisa la’akari da ma’aikatarsa da ma hukumominta a matsayin amintattun abokan hulɗar su na ƙoƙarin daƙile labaran ƙarya da ake yaɗawa kan ayyukan IPMAN.

Ministan ya koka da yadda labaran ƙarya ke yin illa ga ɓangarori daban-daban na al’umma, ya kuma ce akwai fatan alheri ta hanyar haɗin gwiwar ma’aikatarsa da UNESCO na samar da matakan daƙile illolin labaran ƙarya.

Ya yi alƙawarin ba da ƙarin haske ga shirin cikin gida na ƙungiyar mai taken “IPMAN A Yau”, a kan hukumomin yaɗa labarai daban-daban da ke ƙarƙashin ma’aikatarsa.

Idris ya kuma yi alƙawarin yin amfani da tsarin mambobi 30,000 na IPMAN wajen aiwatar da shirye-shiryen sake daidaita darajar da ke ƙunshe a cikin Yarjejeniyar Ƙimar Kasa.

A nasa jawabin, shugaban ƙungiyar IPMAN, Alhaji Abubakar Maigandi Shettima, ya yi alƙawarin ba da goyon baya ga Shirin CNG na shugaban ƙasa, kuma ya yi alƙawarin bai wa gwamnati haɗin kai a cikin shirin samar da makamashin da ba fetur ba, wanda zai ba da ƙwarin gwiwa wajen tabbatar da ajandar Sabuwar Fata ta shugaban ƙasa.

Ya koka kan yadda a kullum ake sarrafa farashin man fetur ta hanyar yaɗa labaran ƙarya tare da neman goyon bayan ma’aikatar domin yaƙar wannan barazana.

Shettima ya ce a nasu ɓangaren, IPMAN ta fito da wani shiri mai taken “IPMAN A Yau” – shirin rediyo da talabijin, wanda zai zama tushen labarai na gaskiya kan ayyukan ƙungiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *