Kungiyar Oxfam ta yi gargadi kan kara yaduwar da cututtuka sakamakon tsananin rashin tsaftataccen ruwa ke yi a Gaza da kuma sokawe da ba a yi gyara kansa ba da ya cika ya ke gudu a kan titunan zirin, kamar yadda kafar watsa labaru ta The New Arab ta ruwaito.
Kamar yadda ta nakalto daga wani nazari na hukumar lafiya ta duniya (WHO), Oxfam ta bayyana cewa kashi 88 cikin 100 na gwajin wani sashin Gaza da aka yi ya nuna cewa ya gurbace da Folio, wanda ke nufin akwai “yiwuwar barkewar cuta sosai.”
Cututtuka masu yaduwa – ciki da gudawa da cututtukan nunfashi, wadanda yanzu sune ke yawan haifar da mace-mace- na karuwa, Inda aka samu masu cututtukan mutum 46,000, mafi yawanci a tsakanin yara, inda ake samun masu cututtukan a duk mako.
Karambau, Kanzuwa da “impetigo” suna kara karuwa nan da nan, musamman a tsakanin jama’ar arewacin Gaza da ke fama da tsananin karancin ruwa.
“Sake samar da ruwa da tsafta na da muhimmanci ga Gaza domin ta dawo daidai bayan watanni 15 na tashin hankali. Dole a tabbatar da tsagaita wuta, mai da kayan agaji a bari su shiga ta yadda Falasdinawa za su iya gina rayuwarsu.” Kamar yadda Clemence Lagouardat, mai kula da ayyukan jin kai na hukumar Oxfam a Gaza, ya bayyana.