DARE ƊAYA ALLAH KAN YI BATURE’: Gwamna Namadi ya bai wa mutum 27 ramcen Naira miliyan 270, domin kama sana’ar zama miloniya

A ƙoƙarin sa na ganin ya cika alƙawarin da ya ɗauka tun farkon hawa mulkin sa cewa, zai buɗa wa mutum 150 hanyoyin kama sana’ar zama miliyoya a zangon sa na farko, Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya bai wa mutum 27 ramcen Naira miliyan 270, domin kama hada-hadar sana’ar zama miloniya.

Wannan lamuni dai na nufin an bai wa kowa Naira miliyan goma-goma kowane.

Gwamna Namadi ya bayyana haka a wurin buɗe taron sanin makamar kasuwanci da tattalin dukiya, wanda aka shirya wa wasu mutum 27, waɗanda aka bai wa bashin, domin su hau dangaramar zama miloniyoyi.

Gwamnatin Jihar Jigawa ce ta ba su lamunin, mai nuni da cewa Namadi ya kama hanyar cika alƙawarin sa na kafa miloniyoyi 150 a faɗin jihar.

An dai zaɓo mutanen 27 ta hanyar ɗaukar mutum ɗaya daga kowace ƙaramar hukuma, cikin ƙananan hukumomin jihar 27.

Malam Namadi ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta samar da miliyoya 27 ta hanyar sana’ar hada-hadar kayan famfon tuƙa-tuƙa, kamar yadda ya yi alƙawarin samar da miloniya 150 kafin shekaru huɗun farko na mulkin sa.

A ta bakin sa, “bayan an yi kyakkyawan nazarin yadda yanayin samar da ruwa ya ke a faɗin jihar nan, musamman matsalar da ta shafi kayan aikin samar da ruwan, gwamnati ta gano cewa akwai matsaloli jingim dangane da rashin kula da dubban famfunan tuƙa-tuƙan da ke faɗin jihar nan.

“Mun gano akwai matsalar rashin wadatar kayan gyara da sinadaran tsaftace ruwa a dukkan ƙananan hukumomin jihar nan.

“Domin magance wannan matsalar, tuni mun bai wa wasu matasa 287 horon yadda ake gyara famfunan tuƙa-tuƙa, kuma muka tallafa masu. Mun ɗauki matashi ɗaya daga kowace mazaɓa ɗaya.

“To daga nan sai muka fito da shirin bai wa mutum 27 ramcen Naira miliyan 10 kowanen su, domin su fara sana’ar sayar da kayan da ake buƙata wajen gina rijiyar burtsatse da kuma kayan gyaran abin da ya lalace na yau da kullum.

“Za su riƙa sayarwa a kowace hedikwatar ƙaramar hukuma 27.”

“Kowane daga cikin su 27, an ba shi jarin Naira miliyan 10, kuma an haɗa shi da masana’antar da ke ƙera kayan domin a riƙa yi masa ragin farashi mai sauƙi.

“Kuma mun umarci kowane shugaban ƙaramar hukumomi ya riƙa sayen kayan gina rijiyoyin burtsatse a hannun su. Kuma ya riƙa ɗaukar matasan da muka horas a aikin gyaran rijiyoyin burtsatse a yankunan su.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *