Gomomin dubunnan masu makoki ne suka taru a filin wasan da ya fi kowanne girma a kasar Lebanon a ranar Lahadi domin halartar jana’izar babban sakataren kungiyar Hezbollah, Sayyid Hassan Nasrallah da magajinsa, Hashem Safieddine, wadanda dukkaninsu Haramtacciyar Kasar Isra’ila ce ta shahadantar da su.
Kamar yadda The New Arab ta ruwaito, taron jana’izar ana kyautata zaton ya kasance daya daga cikin manyan tarukan da aka taba yi a kasar a tarihi a baya-bayan nan, inda mutane suka halarta daga kowanne bangare na Lebanon tare da shigowa Beirut daga akalla kasashe 65, musamman daga wuraren da Hezbollah ke da goyon baya sosai.
Kamar yadda kafar ta bayyana, dubunnai ne ake sa ran zuwansu daga Iran da Iraki, kasashe biyu da ke da yawan mutane ‘yan Shi’a. Sai dai haramta sufurin jirage daga Iran ya sa mutanen Iran bin wasu hanyoyin domin zuwa Lebanon, kamar ta bi ta kasar Iraki.
Taron jama’a da dama ne suka cika filin wasan na Camille Camoun Sports City da titunan da ke zagaye da shi, kamar yadda bayanan jirgi mara matuki ya nuna, suna kada tutar Hezbollah wadda ta ke mai ruwan dorawa da sauran tutoci da suka shafi addini da kasa.
Kakakin majalisar Lebanon kuma shugaban “Amal Movement,” Nabih Berri, an bayyana zai halarci jana’izar. Shugaban kasar Lebanon, Joseph Aoun da Firaminista, Nawaf Salam, za su turo wakilai.
Jagoran harkar Musulunci a Nijeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky, na daya daga cikin malamai da suka halarci taron jana’izar.