Falasdinawa za su iya samar da kasar kansu a cikin Saudi Arabiya – Netanyahu

Firaministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila (HKI), Benjamin Netanyahu, ya sake harzuka mutane bayan shawarar da ya bayar cewa Saudi Arabiya ta samar da kasa domin jama’ar Falasdinu.

Kamar yadda ya ke a cikin wani rahoto na kafar watsa labaru ta Press TV, Netanyahu ya bayyana haka ne a cikin wata hira da ya yi da wani gidan talabijin din HKI a ranar Asabar inda ya ce masarautar “za ta iya samar da kasar Falasdinawa a Saudi Arabiya; suna da kasa mai fadi a can.”

A yayin da ya ke mayar da martani kan wadannan kalamai masu ban mamaki, dan majalisar dokokin Birtaniya a jam’iyyar Labour Party, Afzal Khan, ya bayyana cewa, “Wannan shawarar ta Netanyahu wadda ba kan ka’ida ta ke ba za ta kasance tursasa kwashe jama’a ne da shirin a kakkabe Gaza.”

“Falasdinawa ba su bukatar a sake canza masu wuri. Suna bukatar kasarsu ne kamar kowa.” Kamar yadda ya kara da cewa.

Wata ‘yar majalisar dokokin ta Birtaniya daga jam’iyyar ta Labour, Kim Johnson, ta bayyana kalaman Netanyahu da “marasa ma’ana kuma cin zarafi.”

“Makomar Falasdinu Falasdinawa ne za su tsara, ba wasu daga waje ba.” A cewar Johnson.

“Sakataren harkokin kasashen waje dole ya nuna kin amincewarsa da shawarar Netanyahu da kakkausar murya.” Kamar yadda ta bayyana.

Riyadh ba ta kaiga cewa wani abu ba dangane da kalaman na Netanyahu wadanda ke zuwa bayan shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayar da shawarar mallake Gaza – mai yiwuwa da amfani da sojojin Amurka – domin kirkirar “Yankin bakin teku a Gabas ta tsakiya.”

Tun da farko Trump ya bayar da shawarar cewa Falasdinawa da ke zaune a zirin su sama da miliyan biyu za a iya zaunar da su a wani wurin.

Saudi Arabiya, wadda ke tattaunawa kan daidaita dangantaka da HKI ta hanyar Amurka, ta dakatar da tattaunawar bayan da HKI din ta kaddamar da mummunan yakin ta a Gaza a watan Oktobar shekarar 2023.

Yayin da ta ke mayar da martani a kan kalaman na Trump, ma’aikatar harkokin kasashen wajen Saudi Arabiya ta bayyana a wani rubutun ta a kafar sada zumunta ta X cewa, “Yarima Mohammed bin Salman ya bayyana matsayar masarautar “karara kuma a fili” ta yadda ba a bukatar wata fassara a kowanne hali.”

A cikin jawabin Riyadh ta yi watsi da kalaman Netanyahu cewa daidaita dangantaka “zai faru”, inda suka maimaita matsayarsu na cewa babu dangantaka ba tare da kasar Falasdinawa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *