Gidauniyar USFAH za ta samar da ayyuka ga matasa 50 zuwa shekarar 2027

Gidauniyar USFAH ta gudanar ta taron bayar da fom din jarabawar shiga jami’a wato JAMB kyauta ga matasa har 200 wadanda suka fito daga mazabu 11 na karamar hukumar Sabon Gari da ke jihar Kaduna a ranar 9 ga watan Fabrairun shekarar 2025.

USFAH, wadda gidauniya ce da aka hada sunanta daga ‘Usman’ wato wanda ya kirkiro ta da kuma ‘Faiza’ wadda itace uwargidansa, gidauniya ce da ke da tsare-tsare masu kyau domin ganin cigaban matasa a bagarori daban-daban na rayuwarsu da sauran al’umma.

Taron na wannan shekarar, wanda gidauniyar za ta runka gudanar da shi a duk shekara, ya samu halartar wakilinmu kuma an gudanar da shi ne a kusa da makarantar Sakafatul Islamiyya da ke Hayin Dogo, Samaru Zaria a jihar Kaduna.

Kwamaret Mubarak Usman Jidda daya ne daga cikin jami’an gidauniyar ta USFAH, kuma a cikin jawabin da ya gabatar a yayin taron ya yi bayanin ayyukan gidauniyar daban-daban wadanda duk sun shafi cigaban matasa ne da al’umma baki daya.

Kwamaret Mubarak ya yi bayanin yadda shirin ‘Social Intervention Funds’ na gidauniyar ke taimakawa masallatai da kuma sauran kungiyoyi da kuma shirin gidauniyar na Education Support Initiative wanda a karkashinsa ne aka dauki nauyin daluban domin biya masu kudin jarabawar shiga jami’a ta JAMB, bayar da taimakon kudi ga dalubai, niyyar daukar nauyin karatun dalubai 20 wadanda suka samu maki mai yawa a jarabawar ta shiga jami’a har su gama karatunsu da sauransu.

Usman Baba Kankia shine shugaba kuma wanda ya kirkiro gidauniyar, a cikin jawabin da ya gabatar ya nuna godiyarsa ga al’ummar da suka halarci taron inda ya bayyana cewa, “A wannan shekarar mutum 200 muka dauka, kuma a cikin mutum 200 nan za a cire mutum 20 da suka fi kowa kwazo foundation za ta biya masu registration dinsu daga farko har su gama jami’a da yardar Allah. Bayan registration za mu runka ba su ‘pocket money’ wanda za su runka sawa a aljihu duk wata wanda za su runka sayen takardu, da hawan mashin ko Keke Napep zuwa makaranta in shaa Allahu.”

Shugaban gidauniyar ya bayyana yadda ya samarwa mutane 3 aikin a watanni shida da suka gabata, a satin da ya gabata ya samarwa mutane 15 aikin yi kuma yawanci ‘yan karamar hukumar Sabon Gari ne, kuma satin da za mu shiga zai samarwa mutane 5 aikin yi da yardar Allah, inda ya kara da cewa, “In Allah Ya yarda, ina tabbatarwa iyayena a nan wurin, kafin shekarar 2027, akalla matasan da ke Samaru akalla za su kai mutum 50 wadanda za su samu aikin yi da yardar Allah.”

Shugaban gidauniyar ya kara da tabbatarwa sarakunan da suka halarci taron cewa in damina ta zo za su kaddamar da rabon taki da kayan aiki a karamar hukumar Sabon Gari in shaa Allahu tare da sake bayyana cewa, “Nan da sati biyu za mu raba fom guda 20 na iyayenmu ne mata za mu ba su fom din su 20 akwai wadanda za su koyi dinki, akwai wadanda za su koyi kwalliyar mata, akwai wadanda za su koyi dafa abinci. Kuma idan suka koyi kwas din nan na wata biyu suka gama in dinki ka ka koya za mu tabbatar mun ba ka keken dinki, in ka gama za ka cigaba kai ma ka koyawa wasu.”

A jawabin nasa shugaban ya tabbatar da cewa duk abinda suke yi babu wata manufa ta siyasa, kawai suna yi ne domin su taimaki wadanda ya kamata a karamar hukumar Sabon Gari.

Taron ya samu halartar matasa mata da maza da dama kuma daga cikin manyan bakin da suka halarta akwai uwargidan shugaban gidauniyar Hajiya Faiza, Architect Ibrahim Adamu, Honorable Aliyu Ahmed Manchester, Sarkin Kallon-Kura Alhaji Shehu Musa, Sarkin Bomo Alhaji Mukhtar Salihu, Sarkin Samaru Alhaji Dauda Abubakar, Shugaban Samaru Development Association Dakta Shuibu Muhammad, shugaban jam’iyyar PDP na gundumar Bomo Honorable Bashir Shuibu, shugaban dalubai Kwamaret Adamu Adamu Matazu da sauransu da dama.

An yi addu’ar rufe taron bayan an kammala shi cikin nasara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *