Gwamna Abba ya yi fusata da yadda aikin raba abincin azumi ke gudana a birnin Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano, ya nuna ɓacin ran sa ganin yadda ake tafiyar da aikin dafawa, rabawa da kuma rashin ingancin abincin azumi ke gudana a cikin birnin Kano.

Cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitara ranar Juma’a, Gwamna Abba ya ce bai ji daɗin ganin irin yadda ake dafa abincin ba, sai kuma rashin ingancin abincin.

A wata ziyarar bazata da ya kai a wasu cibiyoyin dafa abinci a ranar Juma’a, a yankin Gidan Maza, cikin Ƙaramar Hukumar Birni da Kewaye, Abba ya kuma nuna ɓacin rai dangane da halayyar masu kula da raba abincin da aikin ke hannun su, waɗanda ya ce tabbas su na ha’intar mabuƙatan da aka ba su amanar dafa abincin domin su.

“Ba za mu amince da aikata rashin gaskiya, algusshu da ha’inci ba wajen kula da dukiyar al’umma. Saboda ya sanar cewa dukkan kuɗaɗen da aka ware domin aikin ciyar da mabuƙata a lokacin azumi, duk a ƙididdige suke na kowace cibiya.” Inji Gwamna Abba.

Gwamnan ya fita aikin duba-garin yadda ake aikin dafawa da raba abincin, bayan samun rahoton sirri cewa ana tafka ƙwange sosai a cibiyoyin raba abinci da dama a cikin birnin Kano.

An dai nuno gwamnan ya na ƙorafi tare da faɗa, yayin da wasu yara ke nuna masa irin abincin da ake raba masu a lokacin buɗe-baki.

Ya yi ƙorafin yadda ake ƙulla wa mabuƙata kunu ɗan tsirit a cikin leda. Sannan kuma an nuno shi ya na ta faɗa kan yadda ake raba shinkafa ba miya, ba kayan haɗin ta, sai dai mai kaɗai aka ƙwalala mata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *